Connect with us

RAHOTANNI

’Yan Sanda Sun Gurfanar da Mutum Hudu Da Laifin Shan Wiwi A Bainar Jama’a

Published

on

Yundunar ‘yan sanda ta gurfanar da Fred, mai shekaru 25 Bakare 29 Salewa mai shekaru22 da kuma Babalola, 25 da cewar suna neman tayar da hankali.
Dansanda mai gabatar da masu laifi Insiffekta Abdulkareem Mustaph ya bayyana wa kotu su wadanda ake zarginsu da aikata lafin, sun aikata laifin ne ranar 30 ga watan Nuwamba, a Tollgate na Ota.
Kamar dai yadda ya ce, su mutanen sun gabatar da kansu a cikin wani halin da bai kamata ba, saboda yin hakan nan iya samar da matsala, saboda sun sha Tabar Wiwi a gaban jama’a, na iya kawo matsala a wurin.
Laifin dai ya saba ma tanaje tanajen sassa na 249 sakin layi na (d) dokokin hana aikata laifi na jihar Ogun na shekarar 2006.
Bayan da aka karanta masu laifukan da suka aikata, sai suka ki yarda da cewar su suka aikata laifin.
Babban majistare Mista Mathew Akinyemi ya yarda da bada belin su, akan kudi Naira t N200, 000 ko wannen su da kuma mutane biyu wadanda kowa sai ya kawo su, a matsayin wadanda za su tsaya masu kafun a bayar da belin su.
Mathew ya bayar da umarnin cewar dole ne wadanda za su tsaya masu dole ne su kasance suna zama a wurin da kotun take, bugu da kari kuma masu aikin yi ne, da kuma shaidar dake nuna sun biya haraji ga gwamnatin jihar Ogun.
Babban majistaren ya dage sauraren karar har sai ranar 21 ga watan Dusamba na wannan shekara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!