Connect with us

RAHOTANNI

Za A Daina Shigo Da Shinkafa Nijeriya A Shekarar 2020 –JKF

Published

on

Ranar Takata ce mai ba Shugaban kasar Ghana shawara akan harkokin tsare -tsare na gidauniyar John Kufor Foundation (JKF) Honorabul Abraham Dwuma ya bayyana cewar yana jin nan da shekara ta 2020 kasar shi za ta daina shigo da shinkafa daga kasashen waje.
Dwuma ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai n cewar (NAN) a Ilorin cewar kungiykr bunkasa noman shinkafa ta Afieka, a karkashin gidauniyar JKF ta samar da wani al’amrin da zai bunkasar harkar noman shinkafa a Afirka.
Ya bayyana cewar dalilin da yasa aka ita cibiyar shine kasashen Afirka a samu wata shekarar da ba sai sun sawo shinkafa ba, daga kasashen waje.
“Shekaru biyu masu zuwa kasar Nijeriya ba tada wani dalili na shigo da shinkafa daga kasashen waje, saboda na yi tafiya wurare masu yawa na ita kasar Nijeriya, inda kuma na gane cewar za su iya yin hakan.
”Jihar Kebbi kadai za ta ita kadai za ta iya samar da shinkafar da za ta ishi Nijeriya, bayan ma ga kuma jihar Sakkwato da kuma Kwara.
“Alal misali a jihar Akwa Ibom suna da filayen da za su samar da shinkafa mai kyau saboda noman shinkafa.
“Lokadin da muka zo Nijeriya manman su, suna suna samu ton daya da rabi, a ko wacce hekta yanzu kuma suna samun ton shida ko wacce hekta, abin da ya linka abubuwan da ake samu sau biyu a shekara daya.
“Muna ganin cewar shi wannan tsarin za a iya cimma shi burin da muke da shi kamar dai yadda Dwuma ya bayyana”.
Ya ce. ita gidauniyar an kafa ta ne saboda sha’awar da tsohon shugaban kasar Ghana John Kufuor, yana da sha’awar cewar manoman nahiyar Afirka suna tafiyar da rayuwar su , ta hanyar noman shinkafa.
“Lokacin da Kufuor ya samu kyautar abinci ta duniya,, bayayana wa ya yi cewar, shi yana ganin ai manoman Afirka ya kamata ace suna da murya daya, idan kuwa har suan da muryar , to yade mu samu hada kansu.
“Don haka da akwai bukartar ayi abin da nake kira hadin kai, a kasashe hudu da suka hada da Ghana, Burkina Faso, Tanzania da kuma Nijeriya.
“Koda yake dais hi wannan tsarin ba wai kawai muna yi ma gwamnatoci maganganu ba, amma su manoma dasu muke da su yi kokari ta wannan gidauniyar su kara bunkasa nagartar abubuwan da suke nomawa, da kuma yawan su da kuma ayyukan su.
Amma kuma a al’amarin da suke idan hara ana bukatar da a tashi tsaye sosai, saboda a tabbatar da ana yin al’amuran kamar yadda ya dace ayi su, su kuma manoman ana ilimantar dasu, su yi abin da ya kamata aba a cikin jahilci ba.
” Abin da muke yi shine muna kirkiro da wasu abubuwa wadanda suka kance tamkar wani gwaji ne, alal misali idan mutum shi mai shigarwa ne, ta hakan za ayi kokari na koya masu abubuwan da suka kamata ga manoma , su kuma manoman, muna yin wasu abubuwam da muke kira su yi al’amarin kamar dai yadda ya dace.
Shi ma da yake fadar ta albarkacin bakin shi Sakatare JanarG ARAP, Alhaji Abdulrauf Lawal, ya bayyana cewar, ita cibiyar ta sa yanzu noman shinkafa ya fara zuwa da sauki, saboda ita kungiyar ta sa noman shinkafa yanzu abu ne mai sauki. Abin ban takaici ne wuna amfani da Naira biliyan daya wajen shigo da shikafa ko wacce rana.
Wannan yana nufin ke nan ana shigowa da shinka fa ta Naira bilyan 365 billion ko wacce shekara, wanda ana yin amfani da kudin, wajen yin wasu abubuwa kamar samar wa matasa ayyukan yi, da kuma kara samar da abubuwan more rayuwa.
“Muna amfani da wadannan kudade masu yawa ne saboda mu shigo dasu, bayan mu kuma muna iya nomawa a gida Nijeriya., akwai shinkafa daban daban, saboda ma harbta noman rani da akwai ta. Za a iya yin hakan idan da akwai yanayi mai kyau da kuma da kuma ruwa mai yawa.
“Da hakan kuma wannan ya nuna ke nan akwai maganar yadda za a noma da kuma maganar gyara shinkafar, sai maganar kai ta kasuwaa sayar da ita , da kuma amfani da ita. Abin za a samu ci gaba kamar yadda ya ce.
Lawal wanda har ila yau shi ne mataimakin shugaba na kasa kungiyar manoman shinkafa ta kasa , ya bayyana cewar kungiyar tana hada kai da rassan ta na jihohi saboda ta taimaka masu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: