Connect with us

LABARAI

Zan Ci Gaba Da Taimaka Wa Ilimi Da Tarbiya -Bala Kofar Nassarawa

Published

on

Tsohon shugaban Kungiyar Ma’aikatan Filaye da Safiyo na Kasa reshen Jahar Kano Alhaji Bala Bello Sulaiman Kofar Nassarawa Kano ya sha alwashin taimakawa harkar Ilimi da tarbiyar al’umma musamman kananan yara da ke makarantun zamani da na addini bisa la’akari da yadda al’ummar mu musamman kananan yara da Matasa da su ke bukatar kyakkyawar kulawa domin samun tarbiya da Ilimin zamantakewa wadda zai kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da fahimtar juna a tsakanin Al’ummar Najeriyar mu ta Yau.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Alhaji Bala Bello wanda yake a matsayin Babban bako me Kaddamarwa domin Tallafawa Makarantar Islamiyya ta Madarasatul Jawahirul Ahbab Litahfizil Kur’anil Kareem da ke Sheka Sabuwar Abuja da ke Karamar Hukumar Kumbotso wacce tayi bikin Walimar yaye Dalibai 15 karo na biyu a Tarihin Makarantar.
Alhaji Bala Bello ya kara da cewa Tarbiyya na bukatar hada karfi da karfe na daukacin Al’umma domin samar da tarbiyya ta gari wanda kuma hakan bata yiyuwa sai da hikima da jajircewa kamar yadda ya kamata, inda kuma ya kawo wata Kissa ta wani Bawan Allah da Dansa anan kusa ba a nesa ba ya ce Yaran yana da matukar himma da san Ilimi to ran nan sai yasamu takardar shaida ta zuwa wata Kasa a wajen Najeriya sai mahaifin ya ce ba zai biya masa ba saboda ba kullum yake samun zuwa Sallar Asiba ba saboda haka indai yana so to sai ya daina fashin zuwa Sallar Asuba cikin Jam’I ya ce tundaga ran nan Yaran bai sake makaraba kullum da shi ake Sallar Asuba cikin Jam’I dan haka tarbiyya na bukatar hikima da tunani mai zurfi. Inda a karshe bayan Jawabinsa ya mikawa Makarantar tallafin Naira 100,000 da kuma alwashin ci gaba da taimakawa wanan Makaranta.
Shi kuwa Babban Malami mai jawabi a wurin Taron Sheik Askiya Sheik Nasaru Kabara wanda yayiwa manema labarai karin haske a wurin Taron ya ce babban abin takaici shi ne a Yau yadda Musulmi suka zama abin tausayi ta haryar nuna gaba da kiyayya a tsakanin su kurum saboda ban bancin mahimta ta Addini dan haka a ko ina a cikin Duniyar mu ta Yau jinin musulmi ake shekarwa a matsayin abinda yafi arha ya ce aikin da wanda ba Musulmi ba zasu ma Musulmi Yau Musulmin ne suke yiwa kansu a tsakanin su, sukuma makiya Allah dan haka ya shawarci Musulmi su hada kansu kamar yadda Ubangiji ya Umarta kasancewar ba wani Musulmi da bai yadda da Kalmar Shahada ba ya kuma yi Nasiha akan zaman lafiya a tsakanin Al’umma Musulmi da ma wanda ba Musulmi ba domin Allah ya hana Ta’addanci da kuma saba dokiki Ubangiji.
Shi ma shugaban Makarantar Malam Usman Abdussalam Ibrahim da shugaban Kungiyar Iyaye da Malaman Makaranta Malam Husain Umar Yakasai yabawa sukayi ga Alhaji Bala Bello kan wannan gudun mawa da Babban Malami Sheik Askiya da sauran Al’umma Maza da Mata da suka taimaka musamman Sakataran Mulki na Kumbotso Honorabul Fesal da ya halarci Taron ya kuma yi alwashin Karamar Hukumar Kumbotso za ta bada tallafi da zarar an rubuta Takardar neman taimakon na Jawahirul Ahbab Kano.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!