Connect with us

MANYAN LABARAI

Zargin Badakala: Ba Ku Da Hurumin Bincikar Ganduje –Kotu Ga Majalisar Jihar Kano

Published

on

A yau Alhamis babbar kotun jihar Kano, ta fitar da hukuncin da yake ce wa majalisar dokokin jihar Kanon ba ta da hurumin gudanar da bincike kan wasu bidiyoyi da ake zargin na gwamnan jihar ne, yana amsar daloli daga hannun dan kwangila ya na zurawa a aljihun babbar riga.

Mai shara’a Ahmad Badamasi ne ya fitar da wannan hukuncin, inda ya bayyana kwamitin mutum bakwai da majalisar ta kafa, da ma majalisar dokokin gaba daya ba su da hurumin gudanar da wani bincike kan zargin badakalar.

Mai shara’ar ya ce maimakon dan jarida Jafar Jafar wanda shine babban editan jaridar shafin intanet mai suna Daily Nigerian, ya fara sakin hoton bidiyon da ya mika su ga hukumar ‘yan sanda ko ta EFCC, ko wata hukumar da take yaki da cin hanci da rashawa, wadanda aikinsu ne gudanar da bincika kan abunda ya shafi cin hanci da rashawan.

Alkalin ya gargadi ‘yan majalisar da su dakata da gudanar da wannan binciken nasu ba tare da yin wata-wata ba, mai shara’ar ya bada misalin hakan a jihohin Kogi da Delta da aka samu badakala makamanciyar wannan, inda kotu ta bayyana majalisar dokokin jihohi basu da hurumin gudanar da binciken badakala a kan gwamnan jiha.

Lauyan majalisar ya ce zai yi magana da wadanda yake karewa don jin ko za su daukaka kara, duk da mun san hukunci mai karfi ne, tunda hukunci ne da ya dogara da dokar kwansitushan din kasa, don haka za su zauna su ga matakin shara’a da ya dace su dauka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!