Connect with us

MANYAN LABARAI

Zargin Basaja: Tsoron Buhari Ya Sa Wasu Sun Haukace –Osinbajo

Published

on

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce, tsoron Shugaba Buhari, yakan jefa wasu mutane cikin yanayi na hauka.
Ya kuma ce, wasu gurbatattun shugabanni sun yi taron dangi a kan Shugaba Buhari, saboda yanda ba ruwan sa da batun cin hanci da rashawa.
Osinbajo yana wadannan bayanan ne a wajen taron kungiyar tuntuba na kwamitocin goyon bayan Buhari, ranar Talata a Abuja.
Ya ce, “Tsoron Buhari yakan sa wasu mutanan hauka. Yanzun sun zo suna cewa, wai shi wani ne mai suna Jubril daga Sudan. Duk ai suna nan a raye a lokacin da Pasto Adeboye, ya je London ya yi masa addu’ar samun lafiya ana kwana guda ya dawo gida Nijeriya. Ta ya wani wai shi Jubril zai rika zama a taron majalisar zartarwa ana tattaunawa da shi, ya kuma rika ganawa da Ministocin sa, a kullum kuma yana yin magana da ni?”
“Dubarar su ita ce: in ka dage a kan fadan karya, wasu suna iya yarda da kai. Buhari ba yana raye ne ba kadai cikin koshin lafiya, da yardan Allah, zai ma yi rayuwa mai tsawo a bayan ya gama zangon mulkin sa na biyu.”
A wajen taron akwai Gwamnan Jihar Legas, Akinwumi Ambode, ya ce, Buhari da Osinbajo, su ne hanyar tabbatar da farfadowar tattalin arzikinmu da bunkasar mu.
Shi kansa Buhari a sa’ilin da yake amsa tambayoyi a kasar Poland, ya yi karin haske gami da karyata batun wai yana yin basaja ne kawai.
Ya ce, gwamnatin ta Buhari ta yi rawar gani ne saboda ba ta tsaya satar kudin al’umma ba; tana yin hanyoyin mota a Jihohin kasar nan 36 ga kuma hanyar Jirgin kasa na tsakanin Legas zuwa Kano, da sauran su.
Osinbajo ya ce, gwamnati tana ciyar da sama da yaran makaranta milyan 9.2 a kullum, ta kuma baiwa kananan masu sana’o’in hannu milyan biyu taimakon da ya inganta rayuwar su ta hanyar shirin ta na ‘Tradermoni,’ ta kuma samawa matasan da suka gama karatun su 500,000 ayyukan yi a karkashin shirin ta na N-Power.
Ya ce, hakan ne ya sanya lalatattun shugabannin baya suka yi masa taron dangi.
“A kullum roka masa mutuwa suke yi. A lokacin da ya dawo da ransa cikin koshin lafiya, sai suka yi ta jimamin hakan, alhalin ‘yan Nijeriya suna ta farin cikin hakan.”
A na shi jawabin, jagoran Jam’iyyar ta APC, Ahmed Tinubu, ya bayyana tabbacin da yake da shi ne na samun nasarar Jam’iyyar ta su a babban zaben shugaban kasa na 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: