Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ya Ki Amincewa Da Kudirin Zabe A Karo Na Hudu

Published

on

Shugaban kasa Buhari ya ki amincewa da kudirin zabe a karo na hudu, bayan da majalisar dattawa ta yi wa kudirin kwaskwarima a cikin shekarar 2018.

Hadimar shugaban kasa a al’amuran da suka shafi majalisun tarayya, Sanata Ita Enang ta ce ta sanar da majalisar matakin kin amincewa da kudirin zaben.

Shugaban kasar ya ki amincewa da kudirin har sau uku a baya, wanda hakan ya fara haifar da cece-kuce, duk da fadar shugaban kasar ta ce akwai kura-kurai a daftarin kudirin karon farko da aka mika shugaban kasar, shiyasa bai sanya hannu ba.

A cikin watan Disamban da ya gabata shugaban kasar ya ki sanya wa kudirin hannu a karo na uku, inda Sanata Enang tace akwai matsaloli a tattare da kudirin, amma bata bayyana wasu matsaloli bane.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!