Connect with us

RAHOTANNI

Mayankar Katsina A Gurbace Take – Bincike

Published

on

Naman da ake yankawa domin ci a dukkanin mayanku manyan garuruwan Jihar Katsina uku, ana yanka shi ne ta hanyar da ba ta dace da kiwon lafiya ba, wani bincike da kungiyar Arewa Trust ta yi ne ya tabbatar da hakan.

Manyan garuruwan sun hada da Katsinan kanta, Funtuwa da kuma Daura.

Wakilinmu da ya ziyarci mayankan ta Katsina, ya tarar da cewa, mahautan sun guji mahautan da aka gina ta shekaru 30 da suka shige, saboda babu mahimman kayan aikin da suka kamata a cikin ta.

Yawancin kayan aikin da aka tanada wa mahautan domun gudanar da aikin na su a cikin tsafta duk a yanzun babu su, shi kanshi ginin wajen ma duk ya lalace.

Manyan dakunan sanyi da ke cikin mayankan duk ba sa aiki, rijiyoyin burtsatsen da ke wajen ma duk sun ruguje, ba kuma ma hasken lantarki a wajen. Mahautan ga su nan duk suna yanka dabbobin na su a harabobin mayankar da ke wajen ginin ainihin ita mayankan kusa da kwatamin da ke fitar da wari mai doyi.

Da bokitai ne ake debo ruwan da ake wanke naman daga wasu rijiyoyi da ke kusa. Wani mahauci mai suna, Hamza Garba yace, da yawan dabbobin da ake yankawa a wajen duk rubewa suke yi.

“A can baya, ana yanka sama da shanu 200 ne a kullum, amma yanzun da kyar muke yanka guda 20,” in ji shi.

Wani mahaucin kuma mai suna Abdullahi cewa ya yi, aikin da ake yi a mahautar sam bai dace da lafiya ba.

“Mun jima da mantawa da wajen a matsayin mayanka ta zamani, saboda yanzun da hannu ne ake yin komai, kamar dai yanda ake yi a zamanin da irin na Kaka da kakanni.”

Jami’in lafiyar kadai da wakilinmu ya cimma a mayankan wasu dalibai ne daga makarantar kiwon lafiya, wanda yace ya zo ne a matsayin koyon aiki kadai.

Wani dalibin da ya amince ya yi magana da wakilin namu a bayan an sakaya sunan sa, cewa ya yi, yanda ake gudanar da aiki a mayankan sam babu kyau.

“Namu a nan kawai shi ne mu gani, mu kuma cika littafan mu da rubutu, amma ba abin da za mu iya yi, lamarin ya sha karfin mu.

Arewa Trust, ta bayar da rahoton cewa, haka ma abin yake a garin Daura, domin har lamarin ya tilasta wa mahautan yin mfani da wasu wuraren na daban domin gyara naman na su.

Wajen da aka gina mayankar ta zamani yana Unguwar Madina ne, a yanzun duk jama’a sun mamaye wajen kowa ya yanki rabon sa.

Haka labarin yake a garin Funtuwa, inda a can din ma aka yi watsi da mayankan, saboda rashin kayan aiki a cikin ta da kuma rashin gyara.

A can din ma haka ake yanka dabbobin da gyara naman na su ta hanyar da ba ta dace da kiwon lafiya ba, wanda hakan ke sanya matukar damuwa ga mazauna a garin.

Masu siyar da abinci suka ce, ba abin da za su iya yi, domin ba su da wata hanyar samun naman da ta wuce wannan a cikin garin.

Suka ce, sukan dai tabbatar da cewa sun wanke naman ne da kyau sosai su kuma dafa shi yanda ya kamata. Madam Franca Ham, wacce ke da kantin siyar da abinci take kuma siyan naman daga mayankan ta ce, takan tabbatar da ta dafa naman ne sosai domin kare lafiyar masu siyan abincin.

Bashir Mohamed, tela ne, ya bayyana damuwar sa da yanda ake yankawa da gyara naman a mayankar da kuma halin da ita mayankar take ciki.

“In har mutum zai je ya gane wa idon sa yanda ake gyara naman a mayankar, yana iya kin cin naman da ya fito daga wajen sam. Lamarin ya kazanta, jini ko ta ina, ga kashin dabbobi nan ko ta ina,” in ji shi. Shugabannin kungiyar mahautan wajen sun ki cewa komi a kan maganan.

Su ma jami’an ma’aikatar noma ta Jihar ba a iya samun gudan su da zai yi magana a kan hakan ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!