Connect with us

RAHOTANNI

Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Ya Zama Cibiyar Noman Wake Mai Yawa

Published

on

Daya daga cikin yankunan da ke cikin jihar Nasarawa  shi ne yankin Auta-Ballrfi, inda yankin a sannu yake zama birni. Yankin na Auta-Ballefi yana daya daga cikin manyan kasuwar sayar da wake, a nan  ana nuna jinjina ga ‘yan gudun hijira da ke suke zama  a kasuwar. Yankin yana da kimanin kilomita 12 daga babban birin tarayyar Abuja daura da babbar hanyar Abuja zuwa Keffi a cikin karamar hukumar Karu da ke cikin jihar, inda wajen ya karbi bakuncin dubban ‘yan gudun hijira da suka fito daga jihar Borno. A ziyarar gani da ido da wakilin jaridar Daily Trust ya kai wa al’ummar, inda  ya tattuna da da wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar da ma fi yawancin suka fito daga garin da ke da nisa kilomita 84 daga Kudu-maso- Yammancin Maiduguri da ke cikin jihar Borno. Kafin ‘yan kungiyar Boko Haram su mamaye yankin a shekarar 2014, ma fi yawancin al’ummar yankin manoman wake ne, inda gonakansu suka kai har zuwa iyakar kasar Chad. Amma bayan tarwatsa yankin da ‘yan Boko Haram suka yi, ma fi yawancin al’ummar yankin da yakin na ‘yan Boko Haram ya daidaita, sun arce ne zuwa garin Abuja, inda suke kwana a cikin bukkoki, kwangaye da kuma tashoshin mota da sauran su. ‘Yan gudun hijirar sun gwammace su zaba wa rayuwarsu mafitar da za ta fishe su don ci gaba da gudanar da rayuwarsu, ta hanyar rungumar noma a gefen garin Abuja inda za a a dinga ba su hayar gonakai.

Mista Philemon Ayuba, ya na daya daga cikin wadannan ‘yan gudun hijira wanda ya zo yankin a shekarar 2015, inda ya ce ya zo yankin ne tare da suaran ‘yan gudun hijira daga garin Gwoza zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar  Nasarawa wasu kuma ‘yan gudun hijirar sun tare a sansanin gudun hijira da ke garin Abuja wasu kuma sun warwasu zuwa wasu wurare don yin aikatau. Ya sanar da cewar hakan ya ba shi kwarin gwiwa inda ya ja ra’ayin wasu ‘yan gudun hijirar suka rungumi noman wake wanda dama shi ne babbar sana’arsu a garin Gwoza kafin farmakin ‘yan Boko Haram. A cewarsa, ya gana da sarakunan gargajiya kamar na Etsu na  Karu, Dagacin kauyen Auta-Ballefi,  malaman addini kamar Archbishop Onaiyekan wanda ya hada su da sauran mahukunta daban-daban don taimakwa ‘yan gudun hijirarsu samu wajen yin noma. Ya ci gaba da cewa, wannan kokarin ya taimaka wajen kafa kasuwar wake ta ‘yan gudun hijira a kauyen  Auta-Ballefi shekara uku da suka shige, inda kuma ake yin dakon sama da manyan motoci dari na wake da ‘yan gudun hijirar suka noma zuwa wasu sassan kasar duk sati nan don sayarwa. Philemon  ya ce, ya zuwa yau, yawan waken da ake kai wa kasuwar yana kara rubanya kuma tare da hadin kan da ‘yan gudun hijirra suke bayarwa, kusan su sama da 8,000, tuni sun mallaki nasu gonakan, inda suka kafa kasuwar tare da biyan harajin naira  150,000 ga karamar hukumar  to Karu duk wata.  Kasuwar ta na daya daga cikin manyan kasuwanni a kasar nan da ake zuwa sayen wake daga garin Ibadan da kuma Enugu, jinjina ga  wannan kokarin na  Philemon wajen binciko ma su sayen waken a daukacin kasar nan. Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar Manama sun sheda wa jaridar Daily Trust damuwarsu da kuma ribar da suke samu saboda rungumar  noman waken don ci gaba da sabuwar rayuwa sakamakon hare-haren na Boko Haram da a baya ya daidaita rayuwar su a jihar Borno.  Wani mai suna Bulus John y koks ne aakan yadda wadanda suka ba su hayar gonan su suke tsallawa masu da tsada, musamman in sunyi girbin mai yawa. A cewarsa, suna yin girbin da ya kai yawan buhunhunan wake  150 a wannan shekarar amma sai dai ya nuna rashin jin dadinsa a kan farashin waken na yanzu da ya ashafi ribarsa. Ya ci gaba da cewa, maganin feshi, takin zamani da kudin hayar gona, inda a karshe muke samun riba yar kadan. Shi ma wani dan gudun hijirar mai suna Albert Peter dan shekara 29 ya ce, mutane da dama sun a zuwa kasuwar don sayen wakensu  a farshin mai sauki, amma a cikin shekara biyu da suka shige, masu sayen waken suna saye daga naira  22,000 zuwa sama , amma yanzu suna son su karyar da farashin zuwa Naira 7,000 na buhu mai dauyen  kilogiram  50. Shi kuwa Zakaria Luka, wanda ya noma buhunna wake 20  kasa da Naira 22,000 na duk buhun wake daya zai ji jiki wajen saun riba domin ya karbo ba shi kafin ya yi noma sa. Shi ma Andrew James dan shekara 33 ya yi hayar gona akan Naira 35,000, inda ya sayi takin zamani, kayan feshi da kuma biyan kudin kwadago, inda a karshe ya samu buhu  21, amma abin da yake ji wa tsaro shi ne yadda kasuwar za ta kasance. Ya yi kira ga gwamnati ta daidaita farashin na wake.  Ministan Noma da raya karkara  Cif  Audu Ogbeh,  ya kai ziyara zuwa kasuwar ta ‘yan gudun hijira, inda  ya ce, ya yi mamaki sosai a kan yan gudun hijirar inda ba su tsaya jiran wani taimako ba suka rungumi noman wake. Ya ce, kasuwar tan a daya daga cikin manyan kasuwanin a kasar nan da ‘yan Nijeriya za su iya dogara da ita duk da kalubalen da manoman suke fuskanata.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!