Connect with us

RAHOTANNI

Sojoji  Sun Tarwatsa Harin Da ‘Yan Boko Haram Suka Kai Bama

Published

on

Al’ummar garin Bama, sun wayi gari a cikin bukukuwan farin ciki ranar Juma’a, bayan da zaratan Sojojin Nijeriya suka fatattaki wata zugar ‘yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, da suka yi yunkurin kutsa kai a cikin garin na Bama.

A cewar majiyar jami’an tsaron, fafatawan da aka yi ta yi da bindugogi a tsakanin ‘yan ta’addan da Sojojin ta ci gaba har misalin karfe 5 na safiya.

“Akwai wani yunkuri da ‘yan ta’adda suka yi na kutsawa cikin garin Bama, da jijjifin safiyar ranar Juma’a, amma zaratan Sojojin mu suka tarwatsa su,” inji majiyar ta jami’an tsaron.

Wani mazaunin garin mai suna, Ajai Mohammed yace, an shiga cikin firgici a lokacin da karan harbe-harbe ya kaure a garin, amma a bayan kimanin awa guda sai abin ya lafa.

“Mun wayi gari a cikin farin ciki, domin an kori ‘yan ta’addan, Sojojin mu sun yi kokari sosai, muna kuma gode masu. Kowa yana cikin farin ciki a yanzun haka,” in ji Ajai.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!