Connect with us

BIDIYO

Ganduje Ya Roki ’Yan Kannywood Su Taya Shi Nema Wa Buhari Kuri’a Miliyan Biyar A Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya roki masu sana’ar shirin fim din Hausa na Kanywood da su taimaka ma sa wajen ganin ya cika alkawarin da ya dauka na kawo wa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, kuri’a miliyan biyar a babban zaben 2019 da ke tafe.

Ganduje ya mika wannan rokon bara ne a lokacin da ya yi ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki na Kannywood a ranar Litinan 3 ga Disamba, 2019 a fadar gwamnatin jihar da daddare.

“Sana’arku ta na da matukar muhimmanci wajen jan hankalin mutane da wayar da kansu. Don haka mu na masu rokon ku da ku je yi ta shirya wakoki da finafinai, don janyo hankalin masu kada kuri’a su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuri’u masu yawan gaske,” in ji Gwamna Ganduje.

Ya kara da cewa, “ku na sane da cewa a nan Kano mun yi alkawarin sama wa Shugaba Buhari kuri’un da su ka fi na kowacce jiha yawa har miliyan biyar. Amma hakan ba za ta samu ba sai da taimakonku da goyon bayanku.

“Saboda haka ku je yi ta fitar da wakoki da finafinai, mu kuma za mu taimaka mu ku wajen shirya su. Kada ku yi kasa a gwiwa.”

Taron dai an shirya ne tsakanin gwamnan da furodusoshi, daraktoci, marubuta, mawaka, jarumai, editoci da sauran masu shirin fim a Kannywood.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!