Connect with us

BIDIYO

Hadaddiyar Kungiyar Kannywood Ba Ta Masaniya Kan Bai Wa ’Yan Fim Rance

Published

on

Babbar Hadaddiyar Kungiyar masu sana’ar shirin fim, Kannywood, wato MOPPAN reshen jihar Kano, ta bayyana korafin cewa, har kawo yanzu hukumar tace finafinai ta jihar a karkashin jagorancin Isma’ila Na’abba Afakallahu, ba ta tuntube ta ba kan batun bashin kudi, don bunkasa sana’ar tasu da gwamnati za ta bayar.

Wannan ikirari ya fito ne daga bakin sakataren hadaddiyar kungiyar masu sana’ar fim a Kano, Alhaji Salisu Mohammed Officer a wata tattaunawarsa da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta wayar tarho.

Bayanai sun nuna cewa, maganar bayar da rancen an jima a na yin nuku-nuku a kanta a na boye wa yawancin masu sana’ar har sai lokacin da wasu masu ruwa da tsaki su ka yi taro na musamman da gwamna, wanda ya kwatsa maganar a wajen taron kuma ya umarci hukumar tace finafinai ta jihar da ta gaggauta samar da tsarin bayar da rancen.

Shi dai rancen gwamnatin tarayya ce ke son bai wa ’yan Kannywood din a tsayin wani tallafin bashi maras ruwa ta hannun Bankin Masana’antu (Bankof Industries). Don haka sai Gwamna Ganduje ya yi alkawarin tsaya mu su a matsayin garanton da zai wuce gaba, don tabbatar da cewa an cika ka’idar karbar bashin.

“Mu dai ba a sanar da mu a kungiyance ba, kuma wannan ne ya sa a ke ta samun matsaloli a masana’antar da gwamnati, saboda mafi yawa ba a su san abinda a ke ciki ba, sai dai su ji labari. Mu kuma da mu ke shugabantar su ba a rubuto ma na ko an tuntube mu ba,” in ji Officer.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!