Connect with us

RAHOTANNI

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Hukunta Jami’anta 28 A Anambra

Published

on

A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan jihae Anambra ta hukunta jami’anta guda 28, bisa laifuka daban-daban wajen gudanar da aiki. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Haruna Mohammed ya bayyana cewa, rundunar ta hukunta jami’anta tare da Koran wadansu daga aiki. Mohammed ya kara da cewa, hukuncin ya biyo bayan dokar da hukumar ta saka na rashin amincewa da cin hanci da rashawa da kuma wasa da aiki. Ya ci gaba da cewa, “Yana daya daga cikin wannan shugabanci na kwamishina Garba Baba Umar a kan rashin amincewa da cin hanci da rashawa da kuma wasa da aiki, shi ya sa ma ya kafa reshe na musamman a jihar Anambra wanda za su binciken wasa da aiki kamar su; kwace, cutar mutane da kuma yin amfani da mukami wanda ya wuce kima.

“Haka kuma, rundunar ta hukunta jami’anta guda 28 bisa laifuka daban-daban na rashin da’a da wadanda aka kora daga aiki da wadanda aka rage musu matsayi da kuma wadanda aka rage wa albashi bisa damfara.”

Hakazalika, kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyana cewa, sama da mutum 124 suka cafke a yankuna daban-daban na jihar bisa laifin shiga kungiyar asiri. Ya kara da cewa, kamen ya gudana ne a wani hari da suka kai a maboyen ‘yan ta’adda. Ya  ce, 37 a cikin wadanda ake zargi sun amsa laifin su, sannan za a mika zuwa kotu, yayin da aka saki 53, a yanzu haka ana binciken 34. Ya kuma kara da cewa, “Kwamishinan ‘yan sanda Garba Umar ya bayar da umurnin kara kai farmaki a maboyen ‘yan ta’adda a cikin jihar, domin a tabbatar da cewa mutane sun gudanar da bikin kisimeti da kuma murnar sabuwar shekara ba tare da wata fargaba ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!