Connect with us

MANYAN LABARAI

Sayen Kuri’a Ne Babban Kalubale Ga Tsarin Dimokradiyyar Kasar Nan  inji Saraki Da Dogara

Published

on

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Mista Yakubu Dogara, sun bayyana cinikin kuri’a da ake fama da shi a yanzu a matsayin babban kalubale ga tsarin dimokradiyyar kasar nan, sun bayyana hakan ne a yayin da suke jagorantar wani shirin jin ra’ayain jama’a kan batun zabukkan shekarar 2019, da aka gudanar yau Litinin a garin Abuja.

Hadakar majalisun tarayya ne suka shirya wannan binciken ra’ayin jama’a daga cikin shirye-shiryen fuskantar kalubalen dake tattare da zabukkan shekarar 2019 da muke fuskanta, a cewar shugabannin majalisun biyu, a daidai lokacin da duniya ta sanyawa Nijeriya idanu don ganin yadda za a gudanar da zabukkan shekarar 2019 din, yakamata a samar da wani yanayi da zai sa kasashen su kalli zabukkan da aminci.

Shugaban kasa Buhari shine shugaban kungiyar kasashen Afirka ta yamma wato (ECOWAS), sannan shugaban hukumar zaben Nijeriya mai zaman kanta (INEC) ne shugaban hukumar zabe ta kasashen Afirka ta yamman, dubi da wadannan mukamai biyu da ‘yan Nijeriya suke rike da, yana nufi duk idon duniya zai zama yana kan Nijeriya ne.

‘A zaben shekarar 2015, kasar mu ta gudanar da zabe na adalci mai cike da inganci, hakan ya sanya sauran kasashen Afirka sun yi sha’awar koyi da yadda muka gudanar da zabukkan mu a shekarar 2015, don haka bai kamata mu bari wannan shaidar da aka mana a shekarar 2015 ta canja zuwa akasin hakan ba, duk abinda muka yi yana zamowa abin koyi ne ga sauran kasashen Afirka, don haka dole mu tashi tsaye don ganin mun tabbatar an sake gudanar da zabukka masu inganci da suka fi na shekarar 2015 ma.’ Inji Saraki

Shugaban kwamitin hukumar zabe na majalisar dattawa, Sanata Sulaiman Nazif ya bayyana wasu dalilai a matsayin manyan dalilan da ya sa ake samun cinikin kui’ar, sune talauci, rashin aikin yi, rashin hukunta wadanda aka kama da laifin cinikin kuri’ar, rashin bin dokar kasa, jahilci da rashin wayar da kan masu kada kuri’a.

Shi kuma shugaban majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara ya bayyana cinkin kuri’ar a matsayin wani nau’I na cin hanci da rashawa mai matukar hadari, duk da abu ne da ya shahara a duniya yadda ake canza ra’ayin masu kada kuri’a, amma fa wannan sabon salon na cinikin kuri’a kai tsaye ta hanyar biyan kudi a take, abu ne mai matukar tada hankali a tsarin dimokradiyya, kuma lallai abu ne da dole a tashi tsaye don yin maganinshi kafin ya zama ruwan dare.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!