Connect with us

RAHOTANNI

‘Yan Sakandare Sun Kashe Dalibi Kan Gasar Siddabaru

Published

on

Wani dalibin sakandare mai suna Kehinde Timilehin dan shekara 17 ya kashe a bokin karatunsa mai Fabour Matthew dan shekara 16, lokacin da suke gudanar da gasar juju. Duka dai yaran guda biyu suna karatu ne a makarantar Ado Grammar School da ke Ado-Ekiti, an dai bayyana cewa, Matthew dan aji biyu ya je jida sai ya dauko gatari ya farmaki Timilehin lokacin da suke gudanar da wannan gasar jujun.

Timilehin dan aji 3 ya rinjayi Matthew inda ya kwace gatarin sannan ya sare shi a kirjinsa, inda ya tafi ya bar shi cikin jini. An zargaya da Matthew zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ekiti da ke Ado-Ekiti, inda a nan ne ya mutu. Bayan mutuwar Matthew, ‘yan kabilar Ebira wadanda suke zauune a kan hanyar Ado-Federal Polytechnic sun kai harin ramuwar gayya ga kabilar Yarbawa da ke yankin. Saboda haka, mafiyawancin iyayen yara ba su bari yaransu sun halacci makaranta ba a ranar Juma’a. Yaran da suka halacci makarantar sun wuya kafin su kawo kafar shi makarantar.

An tura jami’an ‘yan sanda wajen da lamarin ya auku domin su dawo da kwanciyar hankali a yankin, inda aka ijiye su a bakin kofar shigar makarantarShugaban makarantar Mista Ebenezer Falayi tare da matekakinsa Mista Olurotimi Olaoluwa sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2.15 na yamma bayar an tashi daga makaranta. Falayi ya kara da cewa, “Muna bakin ciki da faruwar wannan lamari saboda ya janyo mana rikici. Abin da na ji daga daliban da suke wajen lokacin da lamarin ya auku shi ne, dukkan su biyun suna jayayya a kan shugabanci, inda mamacin ya tafi gida ya dauko makami, sannan shi wanda ake zargi ya yi amfani da wannan makami ya kisan shi. “Sun fada min cewa, wanda ake zargi ne ya kwace gatarin sannan ya sare shi a kirginsa. Ni da malamai da matemakina da kuma rejista wadanda suke makarantar mun garzaya da shi asibitin koyarwa na kami’an jihar Ekiti. Inda muka tsare wanda ake zargin.

“Ya shiga cikin mummunar yana yin, inda daga baya ya mutu. Na yi saure na kira shugaban sashin rundunar ‘yan sanda na Odo-Ado inda ya zo yankin tare da jami’ansa. Mun kuma tuntubi rundunar ‘yan sanda rashen Oke Ila da ke Ado-Ekiti domin su kare wanda ake zargi ga ramowar gayya daga iyalan marigayin. “Mun bukaci jami’an asibitin su gudanar da gwajin game da musabbabin mutuwar kafin su bayar da gawar, amma iyalan mamacin sun ki yarda. “Wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda, ina roko a kara kawo jami’an tsaro a yankin makarantar, domin mun samu labarin cewa, za a kashe dalibai guda 30 a cikin farmakin ranar Juma’a.”

Rundunar ‘yan sanda sun bayyana cewa, an garzaya da wanda ake zargi zuwa sashin rundunar ‘yan sanda masu bincike manyan laifuka. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti DSP Caleb Ikechukwu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa, wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma har an fara gudanar da bincike.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!