Connect with us

LABARAI

Abin Da Ya Sa Na Lashe Zaben 2015 -Buhari

Published

on

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa “Cin hanci da rashawa ya mamaye harkokin kasar nan a gwamnatin da ta gabata kafin shigowar jam’iyyar APC fagen mulkin kasar nan, haka kuma na daga cikin dalilan da ya bai wa jam’iyyar APC nasarar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2015.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a yayin da yake bude taron horarwa na manyan jami’an yaki da cin hanci da rashawa na hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kungiyar tarayyar Afrika ranar Litinin a fadar Shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Buhari ya kuma lura da cewa, “An samu yanayin da cin hanci rashawa ya mamaye kasar gaba daya a gab da gudanar da zaben shekarar 2015 abin kuma ya haifar da gaggarumar matsala a tafiyar da harkokin mulki na gwamnatin da ta gabata .

Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu gwamnatinsa na daukar matakin dawo da matarbar aikin gwamnati da yadda ake gudanar da shi ta yadda aka hana sace sacen dukiyar gwamnati da jami’an gwamnati ke tafkawa.

“A lokacin da muka fara aiki a matsayin gwamnati a watan Mayu na Shekarar 2015, yanayin cin hanci da rashawar da ke gudanar ya kusan hana tafiyar da aikin gwamnati, nasarar da muka samu a zaben da aka gudana ba ya rasa nasaba da irin tawayen da mutane suka yi ga gwamnatin da ta ke tafiyar da kasar a wannna lokacin.

“A watanin da suka gabata mun dauki matakai na dawo da matarbar da mutumcin aikin gwamnati da kuma kawo karshen sace kudaden jama’a a ake yi.

“Amma a bayyane lamarin yake cewa, aikin yaki da cin hanci da rashawa yana da wahalar gaske dom cin hancin da rashawa da sake dabaru da dammarar sake yakin da ake yi masa, mutane kuma na sake canja salon da suke amfana da shi”.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!