Connect with us

MANYAN LABARAI

Ba Za Mu Tattauna Da Amurka Ba –Kwamandan Dakarun Iran

Published

on

Babban kwamandan dakarun juyin-juya hali na jamhuriyyar Musulunci ta Iran, ya ce babu wani dalilin da zai sanya kasar Iran din ta sake zama a teburin sulhu da kasar Amurka, kamar yadda aka yi zaman tattaunawa a baya kan shirin makamashin nukiliyar kasar.

 

‘Masu wannan batun na cewa Iran za ta sake zama a teburin sulhu da kasar Amurka yaudarar kansu kawai suke yi, babu wani dalilin da zai sanya mu sake zama da mayaudara, sannan yakamata su sani kakaba mana takunkumi ba zai sa mu neme sulhu ba da Amurka, su yi ta kakaba mana takunkumi ba abinda zai canja, ba zamu taba saranda ba.’ Inji Mohammad Jafari

 

A watan Oktoban da ya wuce ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Jawad Zarif ya shaida cewa kasar sa ba zata taba zama a teburin shawara da kasar Amurka ba, saboda a cewarshi bai ga dalilin da zasu zauna da masu saba alkawari ba, mayaudara irin Amurka.

 

Wannan matakin da Iran din ta dauka ya biyo bayan ficewa daga yarjejjeniyar makamashin Nukiliya da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi a watan Maris din da ya gabata, sannan ya dauki mayakan kakaba kasar Iran din sababbin takunkumin karya tattalin arziki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!