Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Zayyana Shika-shikan Yaki Da Rashawa

Published

on

A ranar Lahadi ne, Shugaba Buhari ya bayyana mataki na, “A, B, C na yakan cin hanci da rashawa,” a matsayin wani bangare ne na bukin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta Duniya.

Da yake fayyace yanda abin yake a wajen kaddamar da kungiyar, ‘Africa Youth Congress Against Corruption, AYCAC 2018, a fadar gwamnati da ke Abuja, shugaban ya ce matakan na ABC, su ne suke tantance yanda shirin yake, wajen gina al’umma da al’adu, wanda ba za a amince da duk wani abu da zai karya tattalin arzikin kasar nan ba.

Ya ce, “Bari na bayyana maku abin da na yi amanna da shi a matakan na A, B, C, wajen yaki da cin hanci da rashawa; “A” yana nufin yin AIKI ne. Watau za mu daina tsayawa yin surutai, mu shiga aiki kawai.

“B” yana nufin gina gadoji ne. Matasa suna da cikakkiyar daman jagorantar gina gadoji a duk sassan al’ummun su. Sau da yawa, yaki da cin hanci yana bukatar samun hadin kai ne tare da dukkanin abokan tafiya.

“C” yana nufin AL’ADA ne. Hakan na nufin mu yi wa kanmu garkuwa da al’adunmu na Afrika, al’adunmu na kirki da mutunta juna wadanda za su karfafe mu a kan yaki da cin hanci da rashawa. A kan hakan bin diddigi yana farawa ne da ni kaina da kuma kai.

Da yake yabawa shugabannin nahiyar Afrika, Buhari cewa ya yi; “Wannan shekarar ta yakn cin hanci da rashawa ta shugabannin Afrika da jimawa ake nemanta. Shekarar kuma tana cike ne da halayen da za a yi koyi daga juna, alkawurra da kuma abubuwan da ake sa rai a kansu, da kuma wasu labaran nasarorin da aka samu a kan yakin da muke yi da cin hancin da karban rashawa.

Ya ci gaba da cewa, “Ga matasan Afrika, wannan yakin da ake yi da cin hancin da rashawa kune ya kamata ku jagorance shi ku kuma yi nasara a kansa, ta yanda za ku canza yanayin ayyukan da ke karya tattalin arziki a nahiyar ta Afrika.

“Matasa ya kamata su yi amfani da karfin su wajen tabbatar da duk albarkatun kasar mu suna nan a cikin nahiyar ta mu ta Afrika domin amfanar mu, samar da ayyuka da dukiyoyi har ma da samar da ingantacciyan hanyar kiwon lafiyar mu, da ingantaccen ilimi ga al’umman mu. Samun nasarar wannan yakin da ake yi da cin hanci da karban rashawa yana hannunku ne.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!