Connect with us

SIYASA

Gwamna Ganduje Ya Cika Baki Dayan Alkawurran Da Ya Yiwa Kanawa Har Da Kari –Fairus Ibrahim

Published

on

FAURUS MUHAMMAD IBRAHIM, shi ne mataimaki na musamman ga mai girma Gwamnan Kano kan harkokin ma’adanai, jagoran kungiyar gangamin wayar da kan al’umma kan kudurin Buhari da Ganduje (Buhari/Ganduje Mobalisation) matashi na gwagwarmayar tabbatar da nasarar Buhari da Ganduje domin samun nasarar a zaben shekara ta 2019. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA Fairus Muhammad Ibrahim ya bayyana Gwamna Ganduje da cewar shi ne jirgin fiton Kanawa zuwa tudun muntsira, sannan kuma ya alkawartawa Buhari da Ganduje tabbacin yi masu luguden kuri’a  a kakakar zabe mai zuwa. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Yanzu haka ga dukkanin alamu masu zawarcin kujeru iri daban daban kowa ya daura damara ganin hukumar zabe ta kasa ta saki  linzamin fara yakin neman Zabe, shin a Jihar Kano ko wane hali Gwamna da Gwamnatin Ganduje ke ciki?

Alhadulillahi muna kara yiwa Allah godiya bisa baiwar da ya yiwa Gwamna Ganduje da Buhari, musamman ganin yadda akullum jama’a ke  kara amincewa da jagorancin dasu ke kara yi. Mu a Jihar Kano bamu da wani dardar domin jama’a su ne shaidar Gwamna Gaduje, musamman idan aka dubi yadda Gwamnan ya ke kokarin sauya taswirar Kano da Kanawa, sanann kuma ba alfahari muke ba duk Najeriya babu Gwamnan da ya kai Ganduje hidimatawa al’ummarsa.

Ba maganar Aika aika ba, idan dai Magana ake ta ayyukan da ido zai iya gani, hannu ya taba kafa kuma ta taka, nan Kanawa laya tayi kyan rufi. Kuma yanzu a Kano an wuce lokacin da za’a ce Gwamna Ganduje sai ya yi tallan kansa, ko hasidin iza hasada zai baka kyakkyawar shaidar ayyukan Gwamna Ganduje.

 

Wasu na ganin kamar wadannan ayyuka duk kuna yinsu ne sakamakon gabatowar zaben shekara ta 2019, me zaka ce kan haka?

(Dariya) ‘yan Jarida ken an, ana baku kuna ga hannu na, ayyukan Gwamna Gnaduje sun sha banban da na sauran, domin tun lokacin bikin kama aikinsa bayan karbar rantsuwar fara aiki abinda ya fara ambatawa shi ne zai dora kan ayyukan da Kakanni da iyayensa a siyasance suka fara kuma lokaci bai bada ikon kammalawa ba, kuma alhamdulillahi Gwamna Ganduje ya cika wannan alkawari harma da kari. Domin wai ido ba mudu ba yasna kima, al’umma sun gamsu da ayyukan Gwamna Ganduje ba aika aika ba.

Lokaci ba zai bamu damar yin gudu harda zamiya kan ayyukan Gwamna Ganduje ba wanda ya kwararawa Kanawa cikin wadannan shekara uku da rabi masu albarka, amma dai muna yiwa Alah godiya akwai abubuwan da sauran jihohi ma wurinsa suke neman sirrin yadda yake gudanar da jagorancin Kanawa.

 

Ranka yadade akwai bukatar kayiwa mai karatu gwari gwarin wadannan bayanai da kake , kamar rig ace marar wuya ka sanya kamata ya yi kazoo da fashin bakin kalaman naka?

Gaskiya ne amma dai da hausa nake bayanin kuma cikin abubuwan da na ambata wanne ake ganin ya yi kama da kurman baki, da farko yanzu haka doguwar gadar nan wadda ta dara sauran gadojin kasar tsawo Gwamna Ganduje a sume ya sameta, amma yanzu tuni an fara hawa da ababan hawa kafin ma kaddamar da ita, wannan gada itace ta faro tun daga gidan jaridar Triumph ta wuce ta ‘yan Kura, Kasuwar Sabon Gari ta hade da shatale talen Club Road, duk mai shiga Kano ganau ne akan wannan aiki, sannan aikin asbitocin  biyu da tsohuwar Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta fara lokaci ya kure tuni an kammala su harma an fara amfani dasu tare da narka masu kayan aiki irin na zamani.

Gwamnan Ganduje ne Gwamna daya tilo aduk fadin kasar nan wanda bai taba batan watan biyan albashi da hakkuwarn ‘yan fansho ba, kuma alokacin da gwamnoni keta raki kan karin albashin da ake tayin Magana akansa, shi Gwamna Ganduje cewa ya yi ya amince da duk matsayin da aka cimma zai biya ma’aikatan Jihar Kano.

 

Kana Bayani kan manyan ayyuka shin me Gwanatin ta Gnaduje ke yi kan batun matasa wadanda sune kashun bayan kowacce al’umma?

Alhamdulillahi anzo wurin, ina tabbatar maka Gwamna Ganduje yanzu ba sai gobe ba, ba wani Gwamna da ya dauki harkokin tallafawa matasa da himmar gaske kamarsa, yanzu haka zuwan Gwamna Gandu an tallafawa sama matasa dubu 700 maza da mata. Sannan kuma domin a tabbatar da ci gaba da wannan kyakkyawan aiki Gwamna Ganduje ya gina cibiyar koyar da sana’u irinta ta ta farko a kasarnan wadda zata horar da matasa masu yawan gaske a wannan cibiya, kuma gwamnatin Kano zata bayar da tallafi ga ‘yan asalin jihar Kano da suka smau horo a wannan cibiya.

Ba wani bangaren al’umma da a yanzu da Gwamna Ganduje ba tabo ba ta fuskar samar masu da tallafi, acikin makon da ya gabata sama da matasa dubu hudu aka yaye tare da basu jari wadanda suka samu horo irin na zamani kan harkokin wayar hannu taron da aka gudanar a dakin taro na filin wasa na Sani Abacha. Ita kanta mai dakin Gwamna Ganduje Allah ya saka mata da alhairi haka ta ke gudanar da ire iren wadannan taruka da mata kuma ana tayi masu tagomashin alhairi.

 

Yanzu haka akwai kungiyar da kake shugabanta waddat ta mayar  da hankali wajen wayar da kan al’umma kan nasarorin Gwamna Ganduje da Buhari (Buhari/ Ganduje Mobilization) shin mene ayyukan wannan kungiya?

Babu shakka wannan kungiya ce da muka kafa domin ci gaba da wayar da kan al’umma su fahimci kyakkyawar manufofin Gwamantocin biyu, kuma alhamdulillahi mun samar da shugabancin wannan kungiya a daukcin kananan Hukumomin Jihar Kano 44 da kuma sauran mazabunmu a JIhar Kano. Wannan kungiya aikinta shi ne gudanar da taruka tare da bayyanawa jama’a ayyukan da wannan Gwamnati ke kwararawa Kanawa, sanan kuma alokaci guda muna kara hada kan jama’a domin tabbatar da samar da kuri’u masu yawan gaske a zaben shekara ta 2019.

Babu Shaka tsarin kungiyar shi  ne yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarorin Gwamna Ganduje da Buhari, wannan aiki ne da  ya wajaba a wuyan kowa musamman ‘yan asalin Jihar Kano, duba da irin ayyukan alhairi da Gwamna Ganduje ke gudanarwa a Jihar Kana.

 

Wasu na ganin akwai damar  kwace wanan mulki daga hannun gwamnatin ta ku, shin ko me za ka ce kan haka?

Mu daman ai kowa ya san Gwamna Ganduje mutun ne mai kyakkyawan imani mun tabbatar da cewa ba wanda ke da ikon bada mulki ko kwace shi sai Allah, wannan tasa ako da yaushe Gwamna Ganduje Tawussili yake da Allah kuma wurinsa muke nema, hakance mata sa Gwamna Ganduje zabar hidimtawa Kanawa akowane hali ake ciki. Domin kowa yasan har yanzu akwai jihohin dako albashi sai da jibin goshi ake samu. Kuma alhamdulillahi jama’a sun fuskanci kyakkyawar niyyar Gwamna Ganduje. Saboda haka daga cikin ayyukan wannan kungiya akwai kara zaburar da jama’a musamman wajen tabbatar da ganin kowa ya fita wurin zabe kuma ya tabbatar da Gwmna Ganduje, Buhari da sauran ‘yan takarkarunmu na Jam’iyyar APC za’a zaba.

 

Ina batun da ake cewa wani zai nade kafar wando ya dawo domin karbe mulki daga hannun ku?

Ina tabbatar maka da cewa me jiya tayi balle yau, ai wanda ke irin wannan Magana yanzu a Jihar Kano an daina batunsa, kuma yaji ma da rigirmar da ya haifarwa Jam’iyyar tasa, mu a Kano Gwamnan mu Ganduje yana da kyakkyawar tarbiyya wadda itace fitilar da ke nuna nagartar mutum, gashi kuma mai kishin addini da Malamai, masoyin alkur’ani da ahlullahi, saboda haka shi mai waccan Magana tuni ya shiga kusufi a tsarin siyasar Kano, an gama da bangarensa, yanzu jama’ar Kano Ganduje suke Kurunkus.

 

Mene ne Sakonka  na karshe ga Jama’ar da kuke mikawa irin wanna sako na Gwamnatin ta Ganduje?

Alhamdulillahi babban sakona ga Jama’ar Kano bai wuce mukara godewa Allah ba bisa ni’imta Kano da nagrtaccen Jagora mai kishin cigaban Kano da Kanawa, sannan ina kara kira ga jama’a da adaina dauresu da igiyar zato, duk wanda bai san gari ba to ya saurari daka, masu kokarin kawo taskgaro ga ciban Kano ta hanyar farfaganda to muna tabbatar masu da cewa kifi na ganinka mai jar koma, Kanawa Gwamna Ganduje suke da sauran ‘yan takarkarun Jam’iyyar mu ta APC  mai albarka. Muna rokon Allah ya baiwa Gwamna Ganduje da Buhari damar sake dawowa domin ci gaba da ayyukan alhairi ga jama’ar Kano da Kasa baki daya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: