Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Yobe Za Ta Kashe Naira Biliyan 8.7 A Manyan Ayyuka

Published

on

Gwamnatin jihar Yobe ta ayyana kashe naira biliyan 8, 701, 157, 489, wajen gudanar da muhimman ayyukan ci gaba, a zaman majalisar zartswar jihar wanda gwamna Ibrahim Gaidam ya jagoranta.

Wannan furucin ya fito ne daga bakin kwamishinan yada labarai da al’adu,  Alhaji Mala Musti, a lokacin da yake bayyana wa manema labarai sakamakon zaman majalisar, a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu.

Zaman majalisar ya cimma matsaya wajen shimfida hanyoyin mota; bangariri da dama, a babban birnin jihar da waje. Wanda ya hada da ware naira miliyan 560, wajen gina hanyar rukunin gidaje ta Ali Marami, da ke Damaturu- mai tsawon kilo mita 2.8 tare da magudanar ruwa mai tsawon kilo mita 5.6.

Bugu da kari kuma, gwamnatin jihar za ta kashe naira miliyan 187 da yan kai, wajen shimfida hanya mai tsawon kilo mita 2- daga babban titin Maiduguri zuwa karamar cibiyar kamfanin raba wutar lantarki (330KBA-TCN), ta Nijeriya domin saukaka kai-komo a wajen.

Sauran hanyoyin wadanda zaman majalisar ya amince da gunawa, su ne hanyar Unguwar Karo, mai tsawon kilo mita 2.4 da hanyar ruwa, kilo mita 4.8 a birnin Damaturu, wadda kuma za ta lakume naira miliyan 474. Kana da gina hanyar Unguwar Nayi-Nawa; kilo mita 1.5 da magudanar ruwa mai tsawon kilo mita 3 a kan kudi naira miliyan 317, sannan da hanyar Unguwar Abbari da ke Damaturu, mai tsawon kilo mita 1.6 da magudanar ruwa (3.2 km) a kan kudi naira miliyan 360.

A hannu guda kuma, gwamnatin jihar za ta gina hanyar unguwar Njiwaji, mai tazarar kilo mita 3.3 da magudanar ruwa kilo mitk 6.6, wanda za a kashe naira miliyan 749, da doriya wajen shimfida ta.

A gefe guda kuma, gwamnatin jihar za ta kashe naira biliyan daya da yan kai (N1,60,536,098.93) wajen gina hanyar rukunin gidaje ta Don Etiebet, a Damaturu- hanya mai tsawon kilo mita 5.7 tare da magudanar ruwa kilo mita 11.3.

Haka zalika kuma, gwamnatin jihar ta amince da shimfida tagwayen hanyoyi- daga Damaturu, babban birnin jihar, zuwa filin jirgin kasa da kasa (International Cargo Airport) da ke Kalallawa, inda kuma aikin da zai lakume naira biliyan 4.9- domin gudanar dashi.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!