Connect with us

MANYAN LABARAI

Har Yanzu Farashin Litar Man Fetur 145 Ne –PPPRA  

Published

on

Shugaban hukumar da take kula da farashin man fetur ta kasa, Abdulkadir Saidu, ya ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar kara kudin litar man fetur, ana ta rade-radin cewa gwamnatin tarayyar ta na kokarin kara farashin kudin litar man fetur, wanda a halin yanzu ake siyar da shi a Naira 145 lita daya.

Saidu ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da maganar karin kudin litar man fetur din, inda ya ce ba komai bane, illa jita-jita marar tushe balle makama, Saidun ya bayyana hakan ne yau Talata a garin Abuja, sannan ya bukaci ‘yan kasuwa su ma su tabbatar da cewa basu fara tunanin kara farashin ba.

Ya tabbatar da cewa hukumarsu za ta ci gaba da tabbatar da aikinta na ganin farashin litar man fetur din ta tsaya a farashin da gwamnatin tarayya ta bar shi, sannan ya yaba da dillalai da ‘yan kasuwa masu jigilar man fetur din da suka samu cimma daidaito da gwamnatin tarayya kan biyan kudaden tallafin fetur din.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!