Connect with us

MANYAN LABARAI

Jami’an NDLEA Sun Cafke Wani Mutum Da Buhunan Tabar Wiwi

Published

on

Jami’an hukuma mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi sun cafke wani mutum da tabar wiwi da nauyin ta ya kai kilogram 218 da kuma kakin soja na bogi, ana zargin mutumin yana yin sojan gona ne don yin safarar tabar wiwin a tsakanin jihar Neja.

 

Jami’an hukumar sun samu nasarar cafke mutumin ne  a yau Talata, a garin karamar hukumar Makwa ta jihar Neja, inda ya shake buhunan tabar wiwin a bayan wata karamar mota kirar Tayota Kamry, mai dauke da lambar karamar hukumar Makwa ta jihar Neja.

 

Jami’an hukumar sun tsayar da shi don gudanar da bincike a garin Jabba, amma yaki tsayawa, sai suka ci gaba da binshi ba tare da ya san suna biye da shi ba, inda ya tsaya a garin Makwa don cin abinci anan jami’an hukumar su ka samu nasarar cafke shi.

 

Hukumar ta shaida cewa tana kammala binciken ta akan mutumin zata tasa kyayar shi zuwa kotu don fuskantar hukuncin da ya dace da laifinshi, sannan ta bayyana wannan kamun a matsayin babban kamu, saboda yawan tabar wiwin da mutumin ya yi safara ba karamar illa za ta yi ba a cikin al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!