Connect with us

MANYAN LABARAI

Majalisa Ta Biya Dariye Naira Miliyan 85.5 Duk Da Yana Tsare A Gidan Yari

Published

on

Kusan watanni shida kenan da aka tasa kyayar tsohon gwamnan jihar Filato, Cif Joshua Dariye zuwa gidan yari, bayan da babbar kotun Abuja ta same shi da laifin sama da fadi da biliyoyin naira, har yanzu Dariyen yana karbar albashin shi na wata, wanda ya kai Naira 750,000 sai alawus dinshi na wata Naira 13.5.

Bincike ya nuna Dariyen wanda yake wakiltar Filato ta tsakiya a majalisar dattawa, ya ci gaba da karbar albashin shi da alawus na wata-wata, saboda har yanzu majalisar ba ta ayyana kujerar Dariyen a matsayin wacce ba kowa kanta ba, don haka zai ci gaba da amsar kudaden har sai an ayyana kujerar a matsayin wacce ba kowa a kanta.

Dariye wanda tsohon gwamnan jihar Filato ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya shiga hannun hukumar EFCC mai yaki da almundahana da cin hanci da rashawa bisa zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 1.162, inda aka gurfanar da shi a gaban mai shara’a Adebukola Banjoko, wanda ya tasa kyayar shi zuwa gidan yari na tsawon shekaru 10 bayan an same shi da laifi.

Daga cikin hadiman tsohon gwamnan Mista Christopher John, ya ce tsohon gwamnan da hadimanshi suna amsar albashin su da duk alawus din su, Dariyen ya daukaka kara a kotun koli ta Nijeriya, don haka a ka’ida ba za a bayyana kujerar shi a matsayin wacce ba kowa ba, har sai kotun kolin ta tabbatar da daure shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!