Connect with us

LABARAI

Ta Halaka Kanta Da ‘Ya’yanta Don Mijinta Zai Kara Aure

Published

on

Wata mata a kasar Kenya mai suna, Rukia Wasuna, 26, ta kashe kanta tare da ‘ya’yanta biyu ta hanyar cinna wa gidan su wuta a ranar Litinin bayan da ta sami labarin mijinta zai kara aure na biyu.

A cewar tashar talabijin din kasar ta Citizentb, Wasuna, ta kulle yaran ne masu shekaru 6 da 3 tare da ita kanta a cikin daki, sannan ta cinna wa dakin wuta, wanda ke Unguwar Otonglo, na yankin Kisumu.

Da yake tabbatar da aukuwan lamarin, jami’in ‘yan sanda na yankin, Simon Osege, ya ce binciken farko ya nuna cewa matar ta aikata hakan ne a kan sabanin da suka samu da mijin nata.

A cewar jami’in, ta sami labarin mijin nata ne zai kara auren mata ta biyu, da jin hakan ne sai ta garzaya ta siyo fetur daga wani gidan mai da ke kusa sannan ta aikata hakan.

Mista Orwa ya kara da cewa, mijin matan ba shi gida a lokacin da ta aikata aikin, ya tafi Eldoret.

Tuni dai jami’an hana aikata laifuka suka kwashe gawarwakin a matsayin shaida.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!