Connect with us

LABARAI

A Na Ba Sashen Kimiyya Cikakkiyar Goyon Baya–Minista

Published

on

Ministan kimiyya da fasaha Dakta Ogbonnaya Onu, ya yi nuni da cewa za a iya samun ci gaba be idan kn maykr da hknkali a fannin kumiyya da fasaha a tattalin arzikin kasar nan. Onu ya sanar da hakan ne a jawabin sa a lokacin yiwa shagunkn saykr da magunguna guda 43 rijista da aka gudanar a garin Abuja a ranar litinin data wuce. Ya yi nuni da cewa ta hanyar kimiyya da fasaha ne kawai za a iya ciyar da tattalin arzikin kasa gaba. Ya sanar da cewa za a iya rage yawan marasa aiki dake kasar nan idan aka rungumi fannin kimiyya da fasaha kamar yadda kasar China ta yi. Ya yi nuni da cewar in har kasar China zata iya samarwa da yawan alummar ta aiki, ya kamata itama Nijeriya ta rungumi fannin na kimiyya da fasaha sosai don samar da aiki ga yan kasar nan. Ya yi nuni da cewa ta hanyar kimiyya da fasha ne kawai za a itsa auna samun ci gaba, musammam a fannin tattalin arzikin kasa, inda ya ce, in har yawan alummar kasar nan ya ci gaba da habaka akwai babbar matsala in har ba a dauki matakan magance hakan na. Ya sanar da cewa muna ganin yadda matasa masu haurawa ta takun Mediterranean don shiga nahiyar turai suke mutuwa. Acewar sa in har kasar China zata iya samarwa da alummar ta ayyukan yi ya zama wajibi Nijeriya tabi sahunta. Ministan ya ce, yin hakuri shi ne babbkn ginshikin matakin kaiwa ga nasara muna son Nijeriya ta samu wajen gudanar da yin gwaje-gwajen kimiyya inda kowa zai iya nuna tasa hazakar da basirar kimiyya da fasaha. Shi kuwa Darakta Janar na NOTAP, Dakta Dan Azumi Ibrahim ya ce, yawan masu shagunan sayar da magunguna da aka yiwa rijista a karkashin Ministan sun karu daga shida a 2015 zuwa 93 a 2018. Ya ce, taimakon na NOTAP ya karu zuwa 16 a 2016. Ya kuma kara karuwa zuwa 50 a 2017 da kara karuwa zuwa 93 wanda tuni an gabatar 2018. Shugaban na NOTAP ya danganta karin a bisa jagorancin ministan na gari. A taron an karrama jamiar Nsukka da lambobin yabo hudu a bisa kokarin ta a fannin kimiyya da fasaha. Har ila yau, an karrama jamiar Babcock dake Ota da lambar yabo uku, sai da Kalaba ta samu biyu. Sauran sune, ta Jos, Maiduguri, Uyo, ta fasaha da kimiyya ta tarayya dake Owerri, ta kimiyya da fasaha ta tarayya dake Minna, Cobenant dake Ota da kuma cibiyar masanaantu da gudanar da bincike dake Oshodi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!