Connect with us

LABARAI

‘Al’ummar Fagge Sun Nuna Gamsuwa Da Wakilcin Abdullahi Ata’

Published

on

An bayyana tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar Kano, dan majalisa mai wakiltar mazabar Fagge. Hon. Abdullahi Yusuf Ata a matsayin jagora da yake kulawa da ci gaban al’ummar mazabarsa dama jihar Kano baki daya duba da irin ayyukanda yake gabatarwa a yankin.Kansila mai wakiltar mazabar Fagge C. Kwamared Gaddafi Abdullahi Rigo ya bayyana haka.
Yace tsohon kakakin majalisar na jihar Kano ba a taba samun wani dan majalisa da ya wakilci Karamar hukumar Fagge ya ciyar da yankin gaba ba kamarsa, dukkan mazabu 10 na babu wata da ba za ka sami aikinsa, musammam bangaren gina addini shi ya sama ake masa lakabi da Babab mai silar ganin shabbaki khadimul masjid wal’ulama.
Ya ce, dukkan limamai da ladonai da suke karamar hukumar Fagge akwai alawaus-alawus da ake ba su na wata-wata, ba wata mazaba a Fagge da ba za kaga inda ya gina kodai masallaci ko makarantar islamiyya, haka bangare na kyautata wa al’umma sun kai masa mutane yana tallafa musu tun daga kan neman aiki, wa da a kwanannan ya bada takardar daukar aiki ga mutane 47 a KUT cikin irin alfarmarsa.
Gaddafi Abdullahi ya ce, yanzu haka akwai aiki da ake a kwarin akuya a Arewacin Fagge wanda babban titi ne ga kuma aikin kilomita biyar da aka soma lokacin Gwamnatin Kwankwaso an dawo ana yinsa gadon-gadon, dukkan makarantu na Firamare da Sakandire a Fagge babu wacce za ka je ba ka ga ya gina mata block guda hudu ba sama da kasa.
Kansilan na mazabar Fagge C ya ce, duk wanda ke yankin Fagge baya bukatar ayi masa tallar Ata, don gamai tunani da hankali musamman wanda ya damu da addini da son ci gaban Fagge zai zabi Ata don zabensa yi wa addini hidima ne. Mutum ne dake kwatanta dake da riko da addini yake bada gudummuwa na zahiri da badini ta irin tarbiyya da ya samu daga malhaifinsa da malamansa irinsu marigayi Abdullahi Sani Makarantar Lungu da Malam Umar Sani Fagge.
Ya ce, Abdullahi Ata Mutum ne dake kyauta da hannun dama hagu bai sani ba, suda suke yaransa suke tare da da shi sun sha neman a rika yaya ta abubuwa da yake na alkhairi saboda siyasa, amma sai ya ce, a a duk abin da za a yi ayi da ikhilasi sai Allah ya shige gaba akai. Akwai unguwar da yaje yana kakakin majalisar Kano garin Tiga yaga daliban wata makaranta suna karatu a filin Allah ya sa ake yi musu aikin gina makarantar da masallaci yanzu haka ana kan aikin.
Kwamared Gaddafi ya ce, da yardar Allah lokacin zabe kafin wani lokaci sun sami nasarar cin zabe a Fagge, domin duk wanda ya fito yana takara da Abdullahi Ata ya fito ne don bata lokacinsa ba tunaninsa cin zabe ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!