Connect with us

LABARAI

Amurka Ta Dirar Wa Goodluck Jonathan

Published

on

…Ta Ce, Littafinsa Cike Ya Ke Da Karairayi

Ofishin jakadancin Amurka dake Nijeriya ta mayar da martamni a kan zarge dargen da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa Amurka a cikin littafin day a rubuta aka lkuma kaddamar kwanan nan.
Tsohon shugaban kasar, MIsta Jonathan, a littafin day a wallafa mai suna ‘My Transition Hours’ ya yi zargin cewa, tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya sanya hannu a cikin zaben shugaban kasa da aka gudanar na shekarar 2015 inda ya goyi bayan shugaba mai ci yanzu Muhamadu Buhari. Jonathan ya ce, goyon bayan da Obama ya bai wa Buhari a bayana yake inda har sai da ya saki faifan bidiyo in da yake kira da jama’a su bude sabon babi “open a new chapter” ma’ana su zabi sabon shugaan kasa a Nijeriya.
Ya kuma zargi Obama da turo Sakataren kula da kasashen waje na Amurka, John Kerry, zuwa nijeriya in day a yi korafin daga zaben da aka yi a lokacin.
A wata tattauanawa ta kafar sadarwa na zamani ta Facebook wanda wakilinmu ya sa ido a kai, jami’ijn watsa labarai na ofishin jakadancin dake Legas, Mista Russell Brooks, y ace, Jonathan ya shara karya ne a zage zarge ]n day a yi a littafinsa.
Brooks ya kara da cewa, ”An shara karya ne a kana bin da shugaba Obama ko gwamnatinsa ta yi a Nijeriya a gab da kima lokacin zaben 2015. An kasa bayana cewa, burinmu a a lokacin shi ne na Nijeriya ta gudanar da sahihin zabe cikinkwanciyar hankali a sgekarar 2015.
“Amma wasu sun kasa gane dalilinmu na yin duakkan abin day a ace na ganin an guana da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali a shejarar 2019 dake tafe, wannan akida c eta kasa Amurka.
“A shekartun baya, harkar zabe na zuwa da tashin hankali mai dimbin yawa hakan ya sa mutane k eta yekuwar a yi zabe a cikin kanciyar hankali, mun kuma yi imamin cewa, Nijeriya za ta iya gudanar da zaben yadda ya kamata kuma abin da ya faru kenan a shekarar 2015, Nijeriya ta yi zabe mai tsafta. “Lallai an samu mastloli nan da can, kamar dai yadda harkar zabe yake a Nijeriya da ma Amurka, amma an samu gaggarumin ci gaba a zaben da aka gudanar kuma muna da fatan za a karin ci gaba a kana bin da za a gudanar a shekarar 2019.”
Da aka tambaye shi ko kasar Amurka za ta goyi bayan wani dan takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019, Brooks ya ce, Amutka za ta ci gaba da kasance ‘yar baruwanmu a zaben da za a yi gaba daya.
Ya ce, Amurka za ta goyin bayan zaben gudanar da sahihin zabe a cikin gaskiya da kwanciyar hankali ba tare da musgunawa wani ba.
Brooks ya kuma kara da cewa, “Ba ma goyon bayan wani dan takara, ‘yan Nijeriya ne za su yanke hukunci, mu dai muna goyon bayan a gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da musgunawa kowa ba, lallai bama goyon bayan wani dam takara, bama kokarn ganin wani dan takara ya samu nasara, wannnan ba shi ne burinmu ba.”
Daga nan ya kuma bayana cewa, kasar Amurka za ta c gaba da tallafawa hukumar zabe ta INEC da kungiyoyi masu zaman kansu don samun nasarar zabukan dake tafe.
Ya kuma kara da cewa, “Muna tallafa wa Nijeriya ta hanun INEC da kuma ‘yan jarida don a gudanar da zabe sahihi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!