Connect with us

LABARAI

An Bayyana Hanyoyin Bunkasa Noman Masara A Nijeriya

Published

on

Noma na duke tsohon ciniki hausawa suka ce kowa ya zo duniya shi ya tarar haka shugaban kungiyar manoma masara na kasa Alhaji Bello Abubakar Annoor Funtuwa ya bayyana cewar kungiyar su ta manoman masara a Nijeriya tana ci gaba da bunkasa noman masara da kuma karama maniman kwarin gwiwa ta fannin nomansu masara a duk fadin kasar nan.
Alhaji Bello Abubakar Annoor Funtuwa ya yi wannan bayani ne a sallin da wa ansu manyan manoman masara da suka fito daga sassa da banda ban na kasar nan sukazo masa gaisuwar ban girma da kuma neman Karin sanin yanda akeyin noman masara da kuma tallafi na kudi da gwamnati da sauran kamfanoni keba manoman bashi domin karama manoman kwarin gwiwa a wajan noman masarar a karkashin ita wannan kungiyar sannan ya kara da cewar ko a kwanakin baya matasa da sauran manoman masara a cikin garin Zariya kungiyar ta koyama mutane dari uku 300 yanda akeyin dabarun noma domin suma suje sukoyama wadansu kowa ya amfana yara da cewar kuma haka kungiyar take cigaba da zuwa cikin sauran jahohin kasara nan masamman anan Arewacin Nijeriya domin koyama manoman masarar irin wannan dabarun noma saboda kowa ne manomi ya amfana
Sannan kuma yakara da cewar kungiyar a tsaye take a wajen ba manoman shawara kan yanda zasu rikayi a wajan shukar masara da noman tad a kuma zuba mata taki da sauran aiyukanta domin samun nasarar gudanar da wannan shiri a kokarin gwamnati na inganta noman abinci a Nijeriya.
Shugaban ya umurci gwamnati da sauran kamfanoni masamman wadanda suke tallafama harkar noma a Nijeriya dasu cigaba daba manoman masara irin kudin sabulu a kokarin gwamnati na bunkasa aikin noman abinci Allah yayi jagora Amin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!