Connect with us

KASUWANCI

An Bayyana Hanyoyin Magance Matsalolin Samar Da Gidaje A Nijeriya

Published

on

Kwararrun a fannin gudaje a kasar nan sun bayyana cewar, idan aka basu kwarin gwaiwar data dace, zasu taimaka wajen rage matsalar da ake fusknata a kasar na rage matsalolin gidaje, inda suka yi nuni da cewar, akawai bukatar a sanya fannin a cikin manyan ginshikan da ya kamata a samar da dauki akai dom samar da mafita,musamman a kan bin ka’idar da akafi sabawa da ita ta bayar da haya. Manajin Darakta na gidauniyar Family Homes Fund,Mista Femi Adewole, ne ya sanar da hakan, inda ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a baiwa fannin mahimmancin da ya dace don samar da mafita ga matsalolin da ake fuskanta a fannin gannin yadda kimanin mutane miliyan 90 na yan kasar nan, suna dogaro ne a kan dala daya a duk rann. Adewole, wanda ya sanar da hakan a taron bita na kasa da kungiyar gidaje ta kasa ta gudanar ya ce, ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su sani cewar akwai tsada sosai wajen wajen zuba jari a gidaje da ya kamata yan kasa su iya samun saye a bisa sauki. Ya yi nuni da cewa, hukumar gidaje ta kass zata iya samar fa garanti ga masu gina gidaje. Ya bayyana cewa, za’a iya samar da sauye-sauyen da ake bukata akwai kuma bukatar mu samar da cibiyoyi don samar da gidaje a kasar nan. Shi kuma Shugaba kuma jagoran cibiyar kungiyar ta gidaje ta kasa Mohammed Baba-Adamu, ya sanar da cewa, akwai bukatar ayi dubi a kan gina gidaje kuma har yanzu yan kasar nan nada bukatar mallakar nasu gidajen. Ya ce, shin amfanin me muka yi da wannan damar? Munyi magana a kan bukatar da ake da ita na gidaje ba tare da munyi la’akari da yadda za’a samar dasu ba har yanzu kuma akwai gidajen da aka gina a wasu manyan biranen mu kamar Abuja,Legas da kuma Fatakwal da aka gina su a cikin shekaru biyu ba tare da an sayar dasu ba. Ya kara da cewa, mun kuma yi magana a kan karandin kudi na gina gidaje juma har yanzu bamu da usassun kudi da aka ajiye. Ya kara da cewa, mun juma yi korafi a kan tsadar jayan yin gini, kuma tsarin da aka samar don bayar da kwarin gwaiwa ga kayan gini da ake sarrafawa a cikin gida basu samun goyon bayan da ya dace na samar da kyakyawan yanayi ba. Acewar Baba-Adamu, ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki suyiwa fannin garanbawul din da ya dace don kawo karshen matsalar gidaje da ake fama da ita a kasar nan. Ya sanar da cewa, kungiyar tare da AHCN tuni suka samar da hanoyiyin da zasu taimaka don cimma burin samar da gidaje ga yan kasar nan. Sai dai ya koka a kan nauyin da aka dorawa hukumar kula da gine-gine ta jihoyi nauyin gine-gine, I da ya danganta hakan a matsayin wani karin nauyi da bartanar da kudi. Ya ce, ma’aikatar gidaje ya kamata ta rage nauyin dake kanta na wajen samar da tsari da kuma sanya ido a kan tsarin yadda ya kamata don bin kaida. Acewar sa, ya jamata maaikatar gine-gine ta mayar da hankali a kan dokokin muhalli da kuma sanya ido a kan nauyin dake kanta. Ya ce, babu wata tantama akwai bukatar hukumomin kula da gine-gine su tattabatar da ko wanne dan kasa ya samu damar mallakar nasa muhallin tare da goyon bayan gwamnatidin jihohi. Ya yi nuni da cewar wadannan matakan zasu taimaka wajen samar da gidaje a cijin sauki. Shi kuwa shugaban kungiyar masu gina gudaje Mista Ugochukwu Chime, in har an kula da abin yadda ya kamata,za a samu gidaje a cikin sauki, inda har masu tasowa suma zasu iya mallaka. Shima Darakta Janar na Cibiyar bincike ta NBRRI, Farfesa Danladi Matawal ya ce, Nuheriya ta na fama da karancin gidaje Ya yi nuni da cewa, damar da ake da ita na samar da gidaje a cikin sauki. Ya kuma koka a kan yadda ake shigo da kayan gini daga kasashen waje cikin kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!