Connect with us

LABARAI

An Bukaci Gwamnatin Bauchi Ta Kara Himma Kan Inganta Lafiyar Mata Da Yara

Published

on

A taron ta wayar da kai da kuma tattaunawa da kungiyoyi masu ruwa da tsaki kan inganta harkokin kiwon lafiyar kananan yara da mata masu juna biyu a jihar Bauchi Kungiyar mamaye da hadin guiwar ‘yan jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu a Jihar Bauchi sun koka game da yadda ake samun matsalolin kiwon lafiyar kananan yara a Jihar Bauchi saboda abin da ta kira rashin sake kudin hadin guiwa na kashi 15 cikin dari da gwamnatin Jihar Bauchi ta yi alkawari a cikin kasafin kudin ta a zaman shirin inganta lafiya na manufofi bakwai wato (7 Point agenda).
A saboda haka ne kungiyar ta Mamaye Ebidence for Action ta shirya wani kwamiti mai karfi dauke da ‘yan jaridu da kuma kungiyoyin al’umma masu rajin kare lafiya a matakai dabam dabam, inda a kowane watanni uku ake tattaunawa kan batutuwa da kungiyoyin da suke aiki tare don tattaunawa kan matsalolin da suka shafi kiwon lafiya tare da gano yadda za a magance su.
Mista Gideon Foki babban jami’in gudanar da shirin kiwon lafiyar mata masu juna da kananan yara na kungiyar Mamaye Ebidence for Action a Jihar Bauchi cikin jawabinsa a yayin wani zaman tattaunawa da kungiyar ta shirya wa shugabannin kungiyoyi masu bin diddigin kasafin kan harkokin da suka shafi kiwon lafiyar mata da kananan yara da ‘yan jaridun da ake aiki da su a dakin taro na Hazibal da ke titin Yalwa da kuma Chartwell Hotel a Bauchi kwanakin baya, ya ja hankalin jama’a su bayar da goyon baya ga tafiyar kungiyar , haka kuma gwamnati ta tabbatar da sukkan abubuwan da ta alkawarta na inganta lafiya ta cika su.
Inda a karon farko ya ja hankalin gwamnatin Jihar ta Baudhi kan kokarinta na ware kashi 15 cikin dari na kasafin kudi don kashewa sashen kiwon lafiyar mata da yara ya kamata a sa ido wajen ganin komai ya gudana kamar yadda aka tsara don haka ya ce a farko an ci moriyar aikin
lokuta da dama, amma a halin yanzu kuma ana samun tsaiko game da fitar da kudaden don aiki da su.
Ya ce amma kasancewar akwai matsaloli na tattalin arzikin kasa da ake fama da su, a wannan shekarar, kudin sun samu tsaiko basu fito daga aljihun gwamnati ba kamar yadda ya aka saba a wannan shekarar. Don haka ya ja hankalin gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar da ya tallafa wajen ganin ya cika burinsa na inganta rayuwar mata da kananan yara ta hanyar bayar da kudin hadin guiwa da kungiyoyin kiwon lafiya ke aiki da su don ya komai ya gudana kamar yadda ake so.
Gideon Foki ya kara da cewa gaza bayar da irin wadannan kudade yana taimakawa wajen sanya marasa lafiya cikin wahala a yankunan karkara saboda rashin kudin gudanar da ayyuka matukar ba a samu irin wadannan kudade ba daga gwamnati akan lokaci. Don haka ya ja hankalin gwamnatin da ta himmatu wajen ganin tana cika alkawurra game da inganta sashen kiwon lafiya kamar yadda ta saba a baya don a samu ci gaba musamman a yankunan karkara da ake fama da cututtuka da kuma karancin kudi.
Shima shugaban kungiyoyi masu zaman kansu a Jihar Bauchi Mista Jinjiri John Garba cikin jawabin sa ya bayyana cewa kungiyoyi na iya kokari wajen ganin sun bi kadin irin kudaden da ake tanadawa don ganin an tayar da gwamnati daga barci amma a wasu lokutan ganin jami’an
gwamnatin na bayar da wahala don cimma burin ayyukan da aka sa a gaba. Don haka ya ja hankalin kungiyoyin kar su gajiya kan wannan aiki da suke gudanarwa don ganin ana tayar da gwamnatin daga barci a duk lokacin da suka sha’afa da irin alkawurran kudaden da suke yi don
inganta kiwon lafiyar mutanen Jihar Bauchi.
Jagoran ‘yan jaridu masu wayar da kan jama’a Mista Dabid Ayodele, cikin jawabinsa ya bayyana cewa rashin sakin irin wadannan kudade yana haifar da matsala a asibitoci yadda ake samun kungiyoyi masu zaman kan su daga kasashen duniya suna bayar da taimakon sabbin
motocin daukar marasa lafiya da na gudanar da ayyuka, amma rashin kudin gudanarwa a asibitoci yakan sa a ajiye motocin har su lalace saboda rashin mai ko rashin gyaran da bai taka kara ya karya ba.
Yayin da a wasu lokutan kuma rashin bayar da irin wannan kudi na lura da asibitoci ke barazana ga gine ginen asibitocin ko kuma lura da su, A wasu lokutan kuma idan ba a ba direba man da ya dace ba don aiki akan same su a hanya suna daukar fasinja ko kaya don komawa inda suka fito.
A wasu lokutan kuma matsalar gyaran da bai taka kara ya karya ba ke zamowa babban gyara da ke kaiwa ga rufe asibiti ko kuma gaza gudanar da shi yadda ya dace tare da sa ma’aikata cikin wahala.
Don haka Dabid Ayodele ya bayyana cewa kungiyoyi da ‘yan jarida sun wayar da kan mutane musamman mazauna yankunan karkara game da zuwa asibiti don lura da lafiya ko awu da aihuwa kuma an karbi wannan kira amma wasu lokutan rashin bayar da karfin guiwa daga gwamnati yana sa mutane sanyin guiwa yadda sukan yi korafin cewa sun je asibiti basu samu kulawar da ta dace ba don haka ba za su sake komawa ba da makamantan hakan. Ya ce ya zamo wajibi gwamnati idan ta ciza ta hura wajen ganin ana sakin kudin ayyukan kiwon lafiya da ake kasaftawa don ma’aikata su gudanar da ayyukan su cikin walwala da kulawar da ta dace.
Kwamishinar harkokin kiwon lafiya Dokta Zuwaira Ibrahim Hassan cikin jawabanta a kwanakin baya lokacin da kungiyar CISLAC ta kai mata ziyara ofishinta a Bauchi ta bayar da hakuri, kan nuksanin da wannan kudin kiwon laifya ke yi, lamarin da ta bayyana shi akan hakan na faruwa ne saboda karancin kudi da ake fama da shi. Amma gwamnati na hankalce game irin wannan korafi kuma za a magance lamarin nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta saki kudaden da aka kasafta don wannan aiki na kiwon lafiya kamar yadda aka saba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!