Connect with us

LABARAI

An Samu Musayar Ra’ayi A Majalisa Kan Sunayen Sabbin Membobin EFCC

Published

on

An sami sabanin ra’ayi a zauran Majalisar Dattawa, a sa’ilin da ‘yan Majalisar suka sami sabani a kan tabbatar da sabbin wakilai hudu na hukumar EFCC.
Sabbin wakilan su ne, Ndasule Moses, Lawan Mamman, Galadanci Najib da Adeleke Adebayo Rafiu.
A watan Yuli 2016, ne Shugaba Muhammadu Buhari, ya aike wa da Majalisar ta Dattawa, inda yake neman ta tabbatar da sabbin wakilan hukumar.
Shugaban Kwamitin yaki da cin hanci da rasahawa, Chukwuka Utazi, ne ya gabatar da rahoton kwamitin ga ‘yan Majalisun.
Daga nan sai ya bayyana cewa, duk sabbin wakilan sun cancanci mukaman, don haka sai kwamitin ya nemi ‘yan Majalisun da su tabbatar da su.
Tun kafin Majalisar ta fara tattaunawa a kan rahoton Kwamitin ne, Bictor Umeh (APGA, Anambra), ya soki rahoton kwamitin, ya bayyana cewa, duk sabbin nade-naden da aka yi kwanan nan a hukumar, duk ba a yi wa sashen kudu maso gabas nadin kowa ba.
Ya bayyana cewa, a sa’ilin da mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu, ya fito daga sashen arewa maso gabas, shi kuma Sakataren hukumar, daga sashen kudu maso yamma ne ya fito, su kuma sauran mutane biyun da ake neman nadawa duk daga sashen na arewa ne suka fito.
Ya zargi sashen gwamnati da cewa, ba sa bin ka’idar da doka ta ajiye wajen rabon mukaman gwamnati, don haka ya bukaci da a ajiye rahoton tukunna har sai an sake duba yanda aka yi nadin, shawarar da Sanata Eyinnaya Abaribe (PDP, Abia), ya goya wa baya.
A na shi bangaren, jagoran majalisar, Ahmed Lawan, ya bukaci majalisar da ta ci gaba wajen tabbatar da shawarar da kwamitin ya bayar.
Daga nan sai Sanata Ali Ndume, (APC Borno), ya soki kwamitin da rashin yin la’akari da wannan kuskuren da ke cikin rahoton na shi kafin ya bayar da shawarar hakan.
Daganan ne sai Majalisar ta fada cikin hatsaniya, inda ‘yan Majalisun suka tashi tsaye suna nuna junan su suna yi wa juna ihu har na tsawon wani lokaci.
Duk kokarin da shugaban Majalisar, Dakta Bukola Saraki, ya yi na lafar da fusatattun ‘yan majalisar bai yi nasara ba. Hakan ne ya kai ga yin zaman majalisar a cikin sirri.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!