Connect with us

LABARAI

Ba Mu Da Niyyar Karin Kudin Man Fetur –PPPRA

Published

on

Babban Sakataren hukumar sanya farashin mai na kasa, PPPRA, Abdulkadir Saidu, ya ce gwamnatin tarayya ba ta da wani shiri na yin karin farashin man fetur.
Saidu, ya tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja, ya bayyana cewa farashin man yana nan a yanda yake na Naira 145 a kan kowace litar mai guda.
Ya umurci ‘yan Nijeriya su yi watsi da duk wasu rade-radin yin karin farashin na man.
Ya kara da cewa, hukumar ta PPPRA za ta ci gaba da zagayawa tana sa ido a dukkanin inda rumbunan man da gidajen mai din suke a sassan kasar nan.
Ya kuma yi gargadi mai gauni ga duk wani gidan siyar da man da aka kama da saba ka’ida.
Ya kuma yabawa kungiyar ‘yan kasuwan mai ta kasa a kan yanda suka amince da zama a teburin tattaunawa da gwamnatin tarayya domin warware maganan kudaden tallafi da suka biyo gwamnatin ta tarayya.
Ya yi nuni da hukumar ta PPPRA, za ta ci gaba da hada kai da ‘yan kasuwan man wajen tabbatar da tsaftan ma’aikatar man.
Sakataren kuma ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya kokarin da hukumar ta PPPRA ke yi na ganin ba a sami tsaikon samar da man na fetur ba a lokutan bukukuwan karshen shekara da bayan nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!