Connect with us

KASUWANCI

Babban Bankin Nijeriya Ya Janye Tallafi A Kan Shigo Da Takin Zamani

Published

on

A cikin sanarwar da Babban Bankin Nijeriya CBN ya fitar a ranar Litinin da ta wuce, ya saka takin zamani a cikin jerin kayan 41 da haramta shigowa da su cikin kasuwar sayar da hannun jari ta qasar nan. Acewar bankin, zai tabbatar hada-hadar (Fam na M) da ake biyan juxin takin za a biya a ranakun da aka ware. Har ila yau, wata sanarwar ta wani takunkumin shigo da kaya 42 cikin kasuwar ta nuna cewar, bankin ya ci gaba a bisa qoqarin sa na samar da aiki ga masu tasowa da kuma ciyar da qasar nan gaba, a cikin Yulin 2015 bankin ya hana shigo da kaya 41 da xaya cikin kasuwar waxanda za’a iya sarrfawa a cikin qasar nan. Bankin ya ssnar da cewa, tsarin ya taimaka wajen samar da zuba jari da kuma kakkafa masana’antun da a yanzu suke sarrafa kayayaki a cikin qasar nan, inda hakan ya janyo samar da ayyukan yi ga yan qasar. Sai dai bankin ya sanar da cewa, a bisa bayanan da yake samu, ya nuna cewa ana yi wa tsarin hauwan qawara ta hanyar ci gaba da jibge kayan da aka sanyawa takunkumin a cikin qasar nan. Bankin ya yi nuni da cewa, illar ita ce in har ba’a kawo qarshen yi wa tsarin hawan qawara ba, hakan zai iya janyo kasa cimma burin da aka sanya a gaba. Sashen bayanan sirri na bankin tare da haxin gwaiwar EFCC, zasu fara gudsnar da binciken gaggawa a kan asusun ajiyar kamfanoni na bankuna don kawo qarshen karan tsayen da ake yiwa tsarin tare da hukunta dukkan kamfanin da aka samu hannun sa a ciki. A qarshe bankin ya ce, duk bankin da aka samu hannun sa a cikin irin wannan qazamar hada-hadar, za’a qaqaba masa takunkumi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!