Connect with us

LABARAI

‘Correspondents Chapel’ Ta Ziyarci Hukumar Jin Dadin Alhazai Don Inganta Alaka

Published

on

Kungiyar wakilan kafafen sadarwa reshen jihar Bauchi (Correspondents Chapel), ta shaida cewar ta dauki dukkanin matakan da suka dace don yaki da rashin kwarewa a tsakin mambobinta dangane da aiyukan da suke gabansu na jaridanci.
Shugaban Correspondents Chapel a jihar Bauchi, Mista Segun Awofadeji shine ya tsigenta hakan a lokacin da ya jagoranci shugabanin kungiyar kai wata ziyara ga babban sakataren hukumar jin dadin Alhazai na jihar Bauchi a ofishinsa jiya Talata.
Mr Segun Awofadeji ya shaida cewar daukan matakan da suka dace a tsakanin mambobinsu zai basu dama da zarafin tabbatar da kowa na tafiyar da aikin da ke makale a wuyarsa yadda ya kamata domin kare martaba da kimar aikin jarida mai daraje a cikin al’umma.
Shugaban ya shaida wasu daga cikin kalubalen da suke addabar kungiyar wakilan kafafen sadarwa a jihar, inda ya nemi goyon bayan hukumar jin dadin Alhazan domin shawo kansu cikin sauki.
Mista Segun ya shaida cewar ziyarar dai sun yi ta ne domin kara dankon zumunci a tsakanin kungiyarsu da hukumar jin dadin Alhazai domin ganin an samu nasarar kyautata aikin hajji a kowani lokaci.
A lokacin da yake maida jawabinsa, shugaban hukumar jin dadin Alhazai na jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa ya shaida cewar wannan ziyarar ta zo akan gabatar da ta dace, duba da a yanzu haka suna kan gudanar da shirye-shirye da tsare-tsaren gudanar da aikin hajjin shekarar 2019 da ke tafe.
Sakataren ya shaida cewar hukumar jin dadin Alhazai ta kasa da sauran ofisoshinsu na jahohi za su kammala dukkanin tsare-tsare da shirye-shiryensu ne gabanin ranar 15 ga watan Afrilun 2019 da ke tafe ga dukkanin wani shirin tafiya aikin hajjin 2019.
Alhaji Magaji Hardawa ya shaida cewar dukkanin nasarorin da suke samu a hukumar tasu, tana samu ne a bisa gudunmawa da goyon bayan da gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar ke baiwa hukumar.
A bisa hake ne ya nemi hadin kan kungiyar ‘yan jarida reshen wakilan kafafen sadarwa a bisa samun nasarar aiyukansu, ya kuma yaba wa ‘yan jaridar a bisa goyon bayan da suka baiwa hukumar a kowani lokaci, ya nemesu da su daura kan hakan.
Wakilinmu ya shaida mana cewar ziyarar dai ta samu rakiyar shugabanin Kungiyar masu rike da ofisoshi daban daban.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!