Connect with us

MAKALAR YAU

Da Ni Ne Honorabul Sani Aliyu Danlami!

Published

on

Siyasa mugun wasa, idan baka shiga ba, kar ka shiga, idan ka shiga kadda ka fita. wannan shi ne taken da ake yi mata, to amma akwai wani sabon taken da ake yi mata yanzu shi ne, idan ka shiga ka yi abin kirki.
Honorabul Sani Aliyu Danlmai bayan bukatar doguwar gabatarwa a siyasar jihar Katsina, domin a iya cewa shi ne ke rika da siyasa karamar hukumar Katsina kafin masu karfi su nuna masa bai isa ba, amma dalilin haka sun sa zare tsakaninsu da talakawa sai ranar zabe za a gane abin da suke nufi.
Wannan ta sa har gobe babu wani mutun mai farin jinin siyasa a karamar hukumar Katsina kamar Sani Aliyu Danlami, inji wasu hakan baya rasa nasaba da irin takun siyasar da yake yi mai taken kowa naka.
Haka kuma Honorabul Sani Aliyu Danlami ya shiga zukatan jama’a wanda yana da wahalar gaske a iya mantawa da shi ko da kuwa ya bar siyasa, da wahala, a dafa kaza a yada. Koma dai me ke nan har gobe shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Katsina a majalisar tarayya da ke abuja.
A lokacin baya ni da sauran jama’a mun yi kuka har mun gode Allah sakamakon jarabawar da ka shiga ta faduwa zaben fidda gwani da aka gabatar, amma daga baya mun fahimci abin da Allah yake nufi da kai, musamman wani aikin da muka ga yana neman hawa kanka ko ka shirya ko baka shirya ba, na yi wa jama’a hidima a wannan tafiya ta Mai girma gwamna Aminu Bello Masari
Idan da a ce ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami to da akwai abubuwa da daman gaske da yakama in yi, wasu kuma in bari, abin da yasa zan bar su shi ne rashin amfaninsu a siyasa ta, abin da zan yi wasu shi ne amfaninsu ga siyasa da kuma jama’ar da nake tare da su.
Farko dai, inda ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami ya zuwa yanzu na fara gane matsalolin siyasata wanda kowa yana da irin nasa, idan kuma na gano wasu matsalolin to abin da ya rage shi ne yadda zan yi maganinsu cikin sauki tare da taimakon wadanda suka tsaya kai da fata akan al’amarina.
A matsayina na mutun dan adam, ina da wadanda ni kaina na san ina da matsalar siyasa da zamantakewa ta yau da kullin da su, yanzu ne zan daura damarar dinke duk wata baraka da take tsakaninmu da su domin a harkar siyasa yanzu na sa dan ba, damar da ta rage mana ta fi wanda ta kumoce mani, indai da rai da lafiya.
Da ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami da tuni na fara mantawa da wadanda suka sanya ni gaba sai sun ga baya na, tunda ga Allah na dogara amma su kullin suna ta faman sai sunga bayana, wanda ina da yakinin babu ranar da za su yi nasara akan wannan mugun kudiri na su.
Da a ce ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami da rage yawan maganganun siyasa da mutanen da ba su da alaka da siyasata domin suna amfani da wannan damar wajan juya mani zance daga yadda yake zuwa wata manufa ta daban wanda kuma hakan yana kawo mani nakasu a sauran al’amurana na siyasa, na san haka kuma za a ga gyara nan bada jimawa ba.
Kai wallahi inda a ce ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami na tuni na yafewa mutanen da suka fito da rana tsaka suka nuna mani rashin kauna, tunda an haska na ga alherin da ke tafe daman ni mai raba alheri ne, wannan suna kuma ni da shi mutu ka raba insha’Allahu.
Wani abu da nake son jama’a su sani shi ne, gaskiyar magana mun yi rashin jagora abokin tafiya, mun yi rahsin na tare da mu, mun rashin wanda zai hadu da mu cikin mutunci a rabu ana wasa da dariya, mun yi rashin wanda ke daukar kukunmu ya kai wajan gwamna Masari idan abin da ya fi karfinsa, kuma nan take a saurare shi a yi maganin matsalar.
Haka kuma mun yi rashin tsayayye dan gwagwarmayar siyasa da ya rika hana masu kudi barci da ido biyu, mun yi rashin wanda zai cigaba da raba alheri a a wannan hanyar sai dai na san zai cigaba da raba alheri amma ta wata hanyar daban.
Mun yi rashin mutu wanda yake mutun, mun yi rashin daya tamkar da goma, mun yi rashin mutun mai amana, mun yi rashin dan majalisar daya tilo marar wahalar gani, mun yi rashin mutun mai cikar kamalar shugabanci da wakilci. Mun yi rashi mun yi rashi…
Kamar yadda na fada a baya, inda a ce ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami babu abin da zai canza daga irin abubuwan da nake yi wa al’umma na yau da kullin sai dai ya zama dan kadan mai amfani, kuma ba zan sake yarda jama’a su rika kuka da ni ba saboda wadanda nake tare da su ba.
Da a ce ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami duk wasu al’amurana za su koma a bude ma’ana kai tsaye saboda yanzu ta bayyana wasu da suke tare da ni, sun rika zama shinge na jawo mani bakin jini da zagi acikin jama’a, yanzu kuma har sun fara jan jiki za su barni.
Inda ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami da na daina kula masu yi mana hassada da rubuce-rubuce a kafar sadarwa ta zamani, kuma na da jawo duk wanda ke nisa da ni domin kamar yadda na gano akwai rashin fahimta tsakanina da wasu mutane wanda suke amfani da wannan damar wajan aibatani.
Duk da haka wanda duk yasan Honorabul Sani Aliyu Danlami ya san shi tare da mai girma gwamna Aminu Bello Masari wajan tsayawa akan duk lamarin da ya shafi gwamna, to yanzu ma wannan harka zata cigaba fiye da baya, maganganu sun yi yawa akanka Honorabul wasu su ce kaza, wasu su ce an ce ka ce kaza, koma dai me kenan lokaci na zuwa…
Da a ce ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami da na daina tara wadanda suka fadi zabe a gidan akan koma wane irin dalili saboda haka yana haifar da muhawara a tsakanin ‘yan bani na iya, kuma da tuni na canza salon maganata da abokan siyasa, musamman wadanda suke neman sa’a ta kamar wane da wane.
Ni fa da ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami da na sake karatun ta nutsu wajan bude sabuwar kofar jin koken jama’a akaina domin samun bakin zaran warware koma menene, domin ance shawara tafi komi daidaita al’amura.
Da na yi kaina alkawarin cewa a wannan sabuwar tafiya sai na jawo duk wanda ke nesa da ni, musamman wadanda ke tunanin na yi masu nisa saboda siyasa, yana daga cikin shaidar da ake yi masa cewa ya manta da abokansa da suka tashi tare, amma sai nake ganin yanzu lokaci ya yi da za a daina jin irin wannan maganganu.
Da a ce ni Honorabul Sani Aliyu Danlami da tun yanzu zan fara aikina na nemawa gwamna Aminu Bello Masari jama’a akan wadanda yake da su, domin dai a samu nasara a zabe mai zuwa, da sai na tabbatar duk wanda yake goyan bayana kuri’arsa daya bata kauce ba akan gwamna Masari ba.
Abin da nake gani da ni ne Honorabul Sani Aliyu Danlami da tuni na fito da sabbin tsare-tsare na, domin samun damar yin aikin biyu a lokaci guda da tuni na samu wadanda za su kama mani wajan ganin an samu nasara, tunda ita ake nema.
Honorabul Sani Aliyu Danlami har yanzu jama’a da dama na ganin kamar baka canza ba daga yadda kake ba, duk da rashin nasarar da aka samu a zaben fidda gwani da aka yi, akwai bukatar ka zauna ka yi dogon tunani wajan sake tsari da taswirar siyasarka ganin cewa matashi ne kai wanda Allah ya ba dama kuma zai iya sake baka wanda tafi ta baya.
Kadda ka yi fushi da abin da ya faru, kadda ka yi abin da aka yi maka watau ramuwar gayya, kadda ka ce sai ka ga bayan wane, kadda ka cigaba da bayyana sirrinka kamar yadda na san kana yi ga wanda ka yarda da shi, ka cigaba da yin hakuri da jama’a kamar yadda ka saba, ka rika boye fushinka, sannan ka zama mai cika magana da alkawari.
Daga karshe dole ka tashi tsaye wajan gane wanene masoyinka na gaskiya wanene idan kana da shi yana tare da kai, idan baka da shi kuma kun rabo, ka yi kokarin ganin duk wanda kake da matsala da shi, an daidaita kafin gwamna Masari ya kaddamar da yakin neman zabe, ka biya basusuka idan ana binka, ka cika alkawari idan ka dauka, idan duk ka yi wadannan nan gaba kadan zaka gaya duniya abubuwan alheri da suka sameka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!