Connect with us

WASANNI

Dan Wasan Da Real Madrid Da Barcelona Suke Nema Yana Son Barin Lyon

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Lyon, Tunguy Ndombele ya bayyana cewa hukuncin daya dauka na cigaba da zama a kungiyar kwallon kafa ta Lyon yayi daidai sai dai kuma har yanzu zai iya barin kungiyar.
Ndombele, mai shekara 21 a duniya ya ja hankalin manyan kungiyoyin nahiyar turai da suka hada da kungiyoyin Sipaniya, Real Madrid da Barcelona sai kuma zakarar kasar Faransa, PSG da kuma kungiyoyin Manchester City da Eberton daga kasar Ingila.
A cikin watan Agustan daya gabata ne dai dan wasan yakusa barin kungiyar Lyon bayan da manyan kungiyoyi suka fara zawarcinsa sai dai daga baya yaci gaba da zama a kungiyar bayan kungiyar tace bazata siyar dashi ba.
“Hukuncin dana dauka na cigaba da zama a kungiya tat a Lyon yayi daidai domin gashi yanzu ina buga wasanni akai akai kuma nasamu gayyata domin bugawa kasar Faransa wasa saboda haka ina farin ciki da haka” in ji Ndombele
Yaci gaba da cewa “Kungiya ta ba tason siyar dani kuma nima ban takura dole sai na tafi ba kuma gashi muna cin ribar abin domin ina samun buga wasanni sannan kuma itama kungiyar Lyon ina boga mata wasanni.
Sai dai a karshe ya bayyana cewa bai fitar da ran cewa bazai bar Lyon ban an gaba kadan kuma baya tunanin zuwa wata babbar kungiya domin tun yana yaro bai taba tunanin zai buga wasa a babbar kungiya ba saboda haka yanzu duk inda yasamu zuwa zaiyi.
Ndombele dai ya buga wasanni 21 a kungiyarsa ta Lyon kuma ya zura kwallaye biyu a raga sannan kuma a kwanakin baya kociyan kasar Faransa, Didier Deschamp ya gayyace shi inda ya bugawa kasar wasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!