Connect with us

KASUWANCI

FAAN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ta Shiriya

Published

on

Hukumar kula da tashi da saukar jiragen sama ta qasa FAAN ta sanar da cewar ta dakatar da yajin aikin data shirya shiga tashoshin dake Gombe, Kebbi da Bebi saboda ximbin bashin da ya kai Naira miliyan 808.6. Janar Manaja ta sashen bayanai na hukumar Henrietta Yakubu ce ta bayyana hakan, inda ta ce hukumar tq na bin mahukuntan tashar jirgin ta Gombe Naira miliyan 607, 289,972, Kebbi da Bebi tashoshi masu zaman kansu dake Kalaba Naira 124,547,240 da kuma Naira 76,772,948. Ta ci gaba da cewa, mahukuntan tashoshin sun amce da a tattauna bayan da FAAN ta yi barazanar janye gudanar da ayyukan ta. Ta ce, bayan tattaunawar, za su biya bashin, inda ta qara da cewa, shirin shiga yajin aikin da a baya hukumar ta yi niyyar yi, ya zama wajibi don su samu su biya basussukan duk da cewar an ba su waadi. A ranar Lahadin da ta wuce ta ranar 9 ga 2018 hukumar ta baiwa mahukuntan tashoshin takardun wa’adin wata xaya na su biya bashin har a jaridu mun buga na subi umarnin.Ta sanar da cewa, abin zai shafi tashoshi uku kuma matakin waxandan da ake bi bashi zai shafa. Bayan sanarwar, kamfanin jirgin sama na Arik Air ya sanar da cewa, zai dakatar da ayyukan sa a tashoshi Warri da Gombe, inda kuma zirga-zurga a Fatakwal da tashar Murtala Muhammed biyu, da ta Legas za su yi aiki daga babbar filin saukar jirage. Kakakin yaxa labarai na kamfanin na Arik Adebanji Ola a ranar Litinin ya ce, tashin jiragen daga tashoshin Osubi,Warri da Gombe, za su fara tashi a cikin gaggawa, inda kuma ta Fatakwal, an gusa da tashin zuwa MMA2. Bugu da qari, mahukuntan kamfanin Bi-Courtney Aviation Services, masu jiragen sama dake aiki a MMA2, sun sanar da cewa, filin zai kasance a buxe dumin hukumar bata bi su bashi. Hukumar ta yi barazanar dakatar da ayyukan nata ne saboda ta na bin vashin da ya kai Naira Biliyan 1.9. A cikin wasiqar data fitar mai xauke da kwanan wata 30 ga Octobar 2018 zuwa ga kamfanin BASL a kan maganar bashin, maaikatan na FAAN an tura su zuwa filin jirgin na MMA2, inda aka buqaci Kamfanin na Bi-Courtney na ya biya bashin na ayyukan tsaro, kuvutarwa da kuma na kashe gobara da sauran su ko kuma hukumar ta dakatar da ayyukan ta. Sai daia a cikin wasiqar BASL ya gayawa hukumar ta FAAN cewar,duk wani abu da hukumar ko gwwmnati take binsa a cire daga cikin kuxim hukunci Naira Biliyan 132.5 saboda rashin wanzar da yarjejeniyar da aka qulla lda mahukuntan da abin ya shafa. Kamfanin na BASL ya bayar da tabbacin gudanar da ayyukan sa a tashar ta MMA2, ba tare da janyo wata cikas ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!