Connect with us

MANYAN LABARAI

Fadar Gwamnati Ga PDP: Kun Kware A Yada Labarun Karya

Published

on

Fadar Shugaban kasa ta musanta labarin cewa, gwamnatin Buhari, ta kai wani samame a gidan ‘ya’yan dan takarar Shugaban kasa a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ta kwatanta labarin da cewa zuki-tamalle ne.
Babban mai taimakawa Shugaban kasan a kan harkokin manema labarai, Garba Shehu, ne ya fadi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya kuma musanta abin da ya kira da tatsuniyar kulle asusun ajiyar banki na mai rufa wa Atikun baya, Mista Peyer Obi da na iyalansa.
Ya ce, “Ya kamata ya zuwa yanzun ‘yan Nijeriya su nuna damuwar su a kan Jam’iyyar da ba wani abin za ta iya tabukawa a zabe mai zuwa face tafka karerayi da kokarin kautar da gaskiya.
“Abu ne mawuyaci a Nijeriya a halin yanzun a sami wanda ya fi Jam’iyyar PDP iya sharara karya. Shawarar mu a nan ga ‘yan Nijeriya ita ce, a yi biris da su.
A ranar 8 ga watan Disamba ne Jam’iyyar PDP ta zargin cewa an kulle asusun ajiyar banki na mataimakin dan takaran Shugaban kasan ta Peter Obi.

Cikin sanarwar da Jam’iyyar ta fitar ta hannun babban daraktan yada labaranta, Mista Kola Ologbondiyan, ta yi zargin Jam’iyyar ta APC ce da hukumar EFCC, da sanyawa a kulle asusun.
Hukumar ta EFCC dai tuni ta musanta wannan zargin da Jam’iyyar ta PDP ta yi mata. Ta ce ita ba ta da masaniya a kan duk wani abu makamancin hakan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!