Connect with us

SIYASA

Gwamna El-rufai Zai Sake Lashe Zabe -Zannan Jama’a

Published

on

Zannan Jama’a a masarautar Jama’a dake cikin jihar Kaduna State, Alhaji Dankeke Mato ya sanar da cewa, in Allah ya yarda Gwanan jihar Nasiru Ahmad El-Rufa’i zai sake lashe zabe a shekarar 2019.
Zannan ya sanar da hakan ne a hirra sa dajaridar Leadership Hausa a Kadsuna, inda kuma ya danganta za a a sake zabar El-Rufa’I nr saboda kokarin da ya yi wajen ciyar da jihar gaba da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar tun lokacin da ya dare karagar mulkin jihar.
Baasaraken ya ci gaba da cewa, El-Rufa’I ya ciyar da fannonin jihar a gtaba da suka hada da, ilimin zamani, kiwon lafiya, gina hanyoyi samar da tsaro da kuma samar da sauyi a kan yadda ma’aikatan jihar suke gudanar daayyukan su.
Zannan Jama’a ya kuma yabawa gwamnan a kan nada DaktaHadiza Balarabe a matsayin wadda zai yi takara da ita a zaben shekara 2019, inda ya yi nuni da cewa, za ta bayar da gudunmawar da ta dace wajen ciyar da jihar da kuma al’ummar jihar gaba.
Zannan Jama’a a karshe ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar dasu ci gaba da zama lafiya da juna yadda gwamnatin jihar za ta samu sukunin ci gaba da gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!