Connect with us

LABARAI

Gwamnati Da ASUU Sun Kamo Hanyar Yin Sulhu

Published

on

A ranar Litinin ne Ministan kwadago, Dakta Chris Ngige ya bayyana cewa, sun kamo hanyar samun cikkaken fahinta tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar Malaman Jami’a ta kasa ASUU da take yajin aiki a fadin kasar nan.
Ngige ya yi wannnan bayanan ne a taron sasantawa da aka gudanar a Abuja da nufin kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ta tsunduma tun daga ranar 5 ga watan Nuwamba 2018.
Ya kara da cewa, “Mun kammala tattaunawa a yau, ina kuma farin cikin shaida muku cewa, mun tabo bangarori da dama na yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar a shekarar 2017 da nufin gaggauta kawo karshen yajin aikin da ake yi a halin yanzu.
“Mun yi nisa wajen fahintar juna a wasu bangaren yayin da muke kokarin fahintar juna a wasu bangaren.
“A kan maganar rashin isar kudadan albashi a wasu jami’oin gwamnatin tarayya na Ma’aikata da Malamai na jami’oi’n, mun amince cewa, kungiyar ASUU za ta mika cikakken sunayen ma’aikatan da abin ya shafa zuwa ofishin Akanta Janar na Tarayya, an kuma amince kwamimitin shugaban kasa na ‘Presidential Initiatibe on Continuous Auditing’ za su yi nazarin sunayen a ranar Laraba.
“A Saboda haka Akanta Janar zai da wo mana da amsa nan da zuwa ranar Laraba.
“Mun kuma tabo maganar alawus-alawus da sauran sharuddodin da aka cimma a shekrar 2009, mun kuma amince da ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da kuma yadda za mu fuskanci lamarin samar da kudi musamman ganin yadda kudaden shiga yake karanci daga bangaren gwamnati a halin yanzu.”
Ya kuma lura da cewa, taron ya amince a nemo wasu hanyoyi na dabam don sanar da kudaden ci gaba da gudanar da manyan ayyuka na jami’a, an kuma amince da tutubar bangaren gwamnatin da ya kamata don warware sauran matsalolin da suka shafi dalilan yajin aikin da ake yi.
Ngige ya kuma kara da cewa, gwamnati ta shirya don ganin an biya wa malaman jami’o’in bukatunsu da nufin ganin sun koma bakin aiki ba tare da bata wani lokaci ba.
Ya kuma kara da cewa, haka kuma ana kokarin ganin an warware dukkan abin da ya shafi alawus lawasu da aka amince da su, “Mun amince cewa, za mu yi duk abi da ya kamata na ganin an biya dukkan kudaden da ake bi ba tare da takurwa dukkan bangare ba.
“Mun kuma tattauna a kan lamarin jami’o’n jihohi, mun kuma amince da tabbatar da samar wa dukkan jami’o’in kudaden da ya kamata don a samu yaye dalibai masu nagarta daga jami’o’inmu.
“A kan haka ma’aikatar Ilimi za ta kaddamar da kwamitin da zai tattauna da kungiyar gwamnoni don daukar matakan da ya kamata.
Daga nan Ministan ya ce, yana fatan wadannan yarjejeniyar da aka cimma zai sa kungiyar ta janye yajijn aikin da take yi saboda dalibai su samu koma wa makaranta, ya kuma bayyana cewa, an shirya ci gaba da tattaunawar da karfe 4 na yammar ranar 17 ga watan Disamba.
A nasa jawabin, Shugaban kungiyarbta ASUU, Farfesa Abiodun Ogunyemi, ya ce, lallai tattaunawar ta yi matukar amfani.
“A namu bangaren mun saurari alkawurra daga gwamnati kuma za mu kai wa mamboninmu sakon da muka samu sune za su yanke hukuncin abin da za a yi anan gaba,” Inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!