Connect with us

WASANNI

Hazard Ya Ce, Zai Iya Koma Wa Real Madrid

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Eden Hazard ya kara tabbatar da cewar ta yiwu ya koma kungiyar Real Madrid da buga wasa anan gaba idan har y agama yanke hukuncin barin Chelsea.
Har yanzu dan wasan na tawagar kwallon kafar kasar Belgium mai shekara 28 a duniya bai saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zama a Chelsea ba, bayan da kwantiraginsa zai kare a kakar wasa ta 2020.
Hazard bai boye kishirwar cewar, wata rana za ta zo da zai koma Real Madrid da buga wasa ba, kuma ko a baya ya bayyana cewar ya so ya koma Spaniya da buga wasa bayan kammala gasar cin kofin duniya.
Hazard din bai ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Chelsea ba, don sabunta kwantiraginsa a Stamford Bridge, inda ya ce bai yanke shawarar makomar tamaularsa ba a nan gaba amma kuma zai yanke.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nuna karara cewa tanason siyan dan wasan domin yakoma kungiyar bayan ta siyar da dan wasa Cristiano Ronaldo zuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus Chelsea ta kai zagayen gaba a gasar Europa Cup, sannan tana ta hudu a gasar cin kofin firimiya bana kuma kawo yanzu Hazard yanada kwallaye bakwai a gasar firimiya sanann kuma ya taimaka anzura kwallaye da dama.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!