Connect with us

LABARAI

Hukumar Shige Da Fice Ta Karrama Jami’anta 26 Mafiya Kwazo A 2018

Published

on

Ganin cewa karshen shekarar 2018 ya gabato, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta gudanar da gagarumar walimar cin abincin dare tare da mika lambobin yabo ga zakakuran ma’aikatanta da suka fi nuna kwazon aiki a shekarar mai karewa.

Walimar ta gudana ce a shalkwatar hukumar da ke Sauka, a kan hanyar zuwa Babban Filin Jiragen saman Nnamdi Azikiwe na Abuja.

Manyan baki daga takwarorin hukumar da jami’an ofisoshin jakadancin kasashen waje daban-daban suka halarta.

Sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na hukumar, DCI Sunday James ya fitar, ta yi karin hasken cewa, “A sabbin dabarun shugabancin da shugaban Hukumar Shige da Fice Muhammad Babandede ke bullo da su don inganta aikin hukumar, ya yi la’akari da jami’an da suka nuna jaruntaka, kwazon aiki, da’a da fasahar aiki domin ba su lambobin yabo don karfafa musu gwiwa kan sadaukar da rayukansu ga aikin kishin kasa a kan iyakokinmu da cikin rundunar hadin gwiwa na jami’an tsaro a yankin Arewa-Maso-Gabas”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa jami’an hukumar ta shige da fice su ake fara gani a ko wane mashigi na kasar nan a bakin aiki domin karbar baki ko tasa keyarsu su juya da baya kamar yadda aka ba su dama a karkashin dokar shige da fice ta shekarar 2015.

“Walimar cin abincin daren da mika lambobin yabo ga jami’an hukumar ta shekarar 2018 ba kawai ta kunshi shagulgula ba ne, bugu da kari lokaci ne na kara inganta kwazon gwanayen da suka yi bajinta tare da karfafa gwiwar saura su bi sawun wadanda aka karrama”, in ji sanarwar.

Da yake gabatar da jawabi a wurin, Shugaban Hukumar ta Shige da Fice, Muhammad Babandede, ya bayyana cewa daukacin jami’an hukumar sun yi aiki tukuru inda ya jinjina wa goyon bayan da suke samu daga ma’aikatar kula da harkokin cikin gida da kuma hukumar gudanarwar NIS.

“Dama kamar yadda tsarin yake, idan an ciza sai a hura. Yanzu lokacin hurawa ne, shi ya sa muka taru domin wannan biki. A bana mun hukunta jami’anmu da suka zama bata-gari kuma ga shi a yau muna karrama wadanda suka fi yin aiki tukuru. A badi idan Allah ya kai mu, taron zai bunkasa daga walimar cin abincin dare da karramawa zuwa taron bayyana dimbin nasarorin da muka samu a shekara”, in ji shi.

Babandede ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa kawo ci gaba a hukumar irin wadda ba a taba gani ba tun da aka kafa ta.

“Muna gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda amincewa da gudanar da wani aikin da ba a taba ganin irinsa ba a Hukumar Shige da Fice tun da aka kafa ta a shekarar 1958. Tun daga wancan lokacin ba mu taba samun wata cibiyar da za mu daidaita dukkan aikinmu bai-daya ba sai a wannan shekarar da shugaban kasan ya amince da gina Cibiyar Fasahar Tattara Bayanai ta Zamani. A makon da ya gabata, Ministan Cikin Gida (Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau, mai ritaya) ya kaddamar da fara aikin. Wannan fasahar ta zamani idan aka same ta za ta kawo sauyi ga matakan tsaro na Nijeriya. Wakazalika, Ministan Cikin Gida yana tallafa wa hukumar shige da fice sosai tun daga kan aiki na karkashin ma’aikatarsa har zuwa majalisar zartarwa ta tarayya bisa iya shugabancinsa. Haka ita ma hukumar gudanarwarmu. Ba a taba samun wani lokaci da aka kara wa jami’an shige da fice girma ba fiye da shekaru biyun nan (bara da bana)”, ya bayyana.

Muhammad Babandede ya kara da cewa sun mayar da hankali wurin gina sabbin ofisoshi da samar da kayan aiki, inda ya ce sun kudiri aniyar gina akalla manyan ofisoshin hukumar na jihohi guda biyu a ko wacce shekara, yana mai cewar ” a bara mun gina a Kano da Jigawa, a bana za mu kaddamar da guda biyu ranar 17 da 18 ga watan nan a Jihar Abiya da Jihar Filato. Sannan idan Allah ya kai mu badi za mu gina guda shida. Wajibi ne mu yaba wa gwamnati saboda amincewa da samar da wuraren aiki ga hukumar shige da fice”.

Har ila yau, shugaban na NIS ya bayyana cewa ba gine-gine ne kadai suka sanya a gaba ba, suna kuma inganta kwazon jami’an hukumar a makarantunsu na horaswa.

“Idan ka gina ofis kuma ba ka inganta kwazon ma’aikaci ba duk abin da ka yi zai tashi a tutar babu. Don haka muka tsara sabuwar manhajar horaswa da aka fara amfani da ita a makarantunmu na horaswa daban-daban. Farfesoshi shida suka yi aiki tukuru a kan tsara manhajar kuma tuni muka fara ganin alfanunta ta fuskar kwazon jami’anmu”, a ta bakinsa.

Bayan haka, Muhammad Babandede ya ce daga cikin sabbin tsare-tsaren aiki da suka bullo da shi, tsarin ba da takardar izinin shiga kasa a lokacin da bako ya shigo kasa na taimakawa gaya wajen samun falalar zuba jari a Nijeriya, kana ya gode wa ofishin jakadancin Kasar Sin saboda horon da yake taimaka wa jami’ansu da shi.

A nashi bangaren, Babban Sakataren Ma’aikatar CIkin Gida, Dakta Muhammad Umar Tambuwal wanda ya wakilci Ministan Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau, mai ritaya, ya yaba da irin sabbin tsare-tsaren bunkasa aiki da shugaban NIS Muhammad Babandede ke bullo da su, kana ya ce Cibiyar Fasahar Tattara Bayanai ta Zamani da shugaban ya kirkiro da ita, ita ce irinta ta farko a duk fadin Afirka. Ya nemi sauran shugabannin takwarorin hukumar su yi koyi da shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa NIS za ta ci gaba da samun goyon bayan ma’aikatarsu domin ayyuakanta su kara bunkasa.

Daga bisani dai an mika wa jami’an hukumar su 26 lambobin yabo kan kokarin da suka yi a bakin aiki a matakai daban-daban da suka hada da kwazo, iya shugabanci, jaruntaka da sauran su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!