Connect with us

LABARAI

Hulda A Kasuwar Hannun Jari Ya Ragu A Wannan Makon

Published

on

A bisa fashin bakin da aka yi na sati-sati a kasuwar sayar da hannun jari ta kasa,ya nuna cewar an samu ragi a cikin satin inda ya sauka da kashi 7.67 bisa dari a satin da ya wuce ya kuma kara sauka zuwa kashi 8.05 bisa dari a karshen hada-hadar da aka yi a kasuwar ta ranar litinin data wuce.
A cikin rahoton sati da kasuwar ta fitar ta bayyana cewar, an samu ribar ehiya data kai biliyan 1.107 billion daidai fa naira biliyan 11.192 na hada-hada guda 14,430 da aka yi a kasuwar a satin da ya gabata wanda masu zuba jari suka zuba sabanin jimlar shiyar data kai biliyan 1.199 da aka kiyasta kudin ya kai maira biliyan 14.277 da aka yi hada-hadar data kai 15,841 a wancan satin.
Ribar da aka samu a ranar jumaa an sake mayar da ita a ranar litinin gani cewar dukkan shiyar, ta fadi zuwa kashi 0.82, inda aka kulle a kan 30,614.73 da kuma naira tiriliyan 11.176.Kokarin da aka yi a daukacin fanonin an samu nakasu. Kayan sayarwa sun fadi da kashi 2.32 bisa dari saboda matsin lambar kamfanin Nestlé Nigeria Plc, Nigerian Breweries Plc da kuma UACN Plc. Fannin mai da iskar Gas, ya kai kashi 1.19 bisa dari saboda asarar da kamfanoni 11 Plc da kamfanin Oando Plc suka yi.
Har ila yau, fannin inshora nan ma an samu raguwa da kai kashi 0.74 bisa dari saboda an dauki riba daga Kamfanin Cornerstone Insurance Plc da Mutual Benefits Assurance Plc. A fannin bankuna kuwa,an samu raguwar data kai kashi 0.39 bisa dari na ribar da aka dauka daga bankin Zenith Plc, Stanbic IBTC Holdings Plc da kuma Guaranty Trust Bank Plc. Kayan masanaantu da aka sarrafa ragu da kashi 0.25 bisa dari saboda faduwar farashi na shiyar Kamfanin Lafarge Africa Plc.
Kaya sha hudu kuma sun samu tagomashin farashi sabanin 25 da suka yi asarar data kai 0.6d. Manya biyar dk suka tabka asara sune, Trans-nationwide Edpress Plc, Forte Oil Plc, Bitafoam Nigeria Plc, Sterling Bank Plc da kuma United Bank for Africa Plc, wadanda shiyar su ta kai kashi 8.47 bisa dari, kashi 6.39 bisa dari, kashi 5.52 bisa dari 3.57 da kuma kashi biyu bisa dari. Har ila yau, manya biyar da suka tabka asara sune, Libestock Feeds Plc, Cornerstone Insurance, Mutual Benefits, 11 Plc da UACN, wadanda farashin shiyar su baki daya ta sauka zuwa kashi 9.62 bisa dari, kashi 9.09 bisa dari, kashi 8.70 bisa dari 8.47 kashi bakwai bisa dari. Masu yin fashin baki a kamfanin Meristem Securities, sun bayyana cewar, kokarin da aka yi a kasuwar ta janyo raguwar samun riba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!