Connect with us

WASANNI

Idan Messi Ya Isa Shi Ma Ya dawo Seria A, Inji Ronaldo

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya kalubalanci takwaransa na Barcelona Lionel Messi kan sauya sheka zuwa daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafar Italiya kamar yadda ya yi.
Ronaldo mai shekaru 33 ya ce yana fata watarana Messi ya sauya ra’ayinsa na kare kwallon kafarsa a Sipaniya don gwada wani bangare na duniya daban, a cewarsa ta hakan ne za a kara gane kwazonshi.
Ronaldo da Messi mai shekaru 31 wadanda suka shafe tsawon kusan shekaru 10 suna lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or har yanzu na a matsayin ‘yan wasa biyu da babu kamarsu a duniyar kwallo.
Sai dai Ronaldon dan Portugal wanda ya koma Juventus daga Real Madrid kan yuro miliyan 99 a wannan kaka bayan shafe shekaru 9 a kungiyar, ya ce sai dan wasa ya gwada sa’ar sa a kungiyoyi daban-daban ne za a gane kwazon a tare da shi ne ba wai a tare da kungiyar sa ba.
Ronaldon wanda ya gwada sa’arsa a Ingila da Sipaniya yanzu kuma ya ke buga wasansa a Italiya ya ce ya karbi kalubale wajen sauya sheka kuma ya na fatan Messi ma zai karba, amma idan har yana farin ciki a Barcelonar sa kamar yadda ya ke yi a baya, to yana masa fatan alkhairi.
Messi dai ya jaddada cewa yana farin ciki a kungiyarsa ta Barcelona kuma bashi da niyyar barin kungiyar domin buga wata gasa a nahiyar turai inda yace idan yabar Barcelona kasarsa ta Argentina zai koma domin yaci gaba da buga wasans acan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!