Connect with us

KASUWANCI

Jama’ar Jihar Abia Suna Qorafin Watsi Da Su Da Kamfanin NNPC Ta Yi

Published

on

A ranar Litinin da ta wuce al’ummar yankin Okpokoroala Uratta, dake cikin qaramar hukumar Osisioma Ngwa a jihar Abia suka janyo ayyuka suka tsaya chak a defo xin Kamfanin NNPC dake Aba a bisa zargin da suka yi na cewar kamfanin ya yi watsi dasu. Alumar sun bayyana koken su ne ta hanyar yin zanga-zanga, inda suka kulle qofofin shiga defo xin suka nuna buqar suna son ganin chqnji na ainahi daga mahukuntan kamfanin saboda mayar dasu da akayi saniyar ware. Zanga-zangar ta firgitar sosai ganin cewar, wani bokan su da shi ne ya jagoranci dubban matassla zuwa zanga-zangar ya kafe wata sandar sa ta bokanci a gaban qofar shigar defo, ya kuma qalubalanci duk wani ma’aikaci a defo xin in ya isa ya shiga cikin harabar defo xin. Masu zanga-zangar suna xauke da kwalaye dake xauke da rubutun koken su kamar haka,‘NNPC ki tuna da alummar dake kewaye dake, ‘NNPC tun shekarar 1979, baka tava tallafa mana koda da allurar ofis ba mun gaji da watsin da kuka yi damu. Masu zanga-zangar sun ta rera waqiqin yaqi sai dai sun gudanar da zanga-zangar ce a cikin lumana a gindin qofar ta defo. A jawabin sa a madadin alummar yankun, shugaban alummar ta Uratt Young Ngwaziem ya ce, yarjejeniyar da muka qulla da kamfanin ayyuka 60 dole ne suje ga alummar yankin. Acewar sa, manyan kamfanin suna cike makwafin maaikatan kamfanin ne da yanuwansu na ayyukan da aka ware don alummar yankin. Mutum xaya namu da yake yin aiki a kamfanin tuni an cire shi. Ya sanar da cewa, kamfanin ya karve mana filayen mu ba tare da bamu diyya ba kuma hnyar ma ta shiga defo, kamfanin ya kasa gyra ta. Ya ce, bama damun su, inda hakan ya sanya suke yi mana kallon wawaye. Shi kuwa shugaban matasan yankin Okpokoroala Chukwuemeka Chidi ya yi nuni da cewa kamfa kamfanin na NNPC a yankin bai amfane su da komai ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!