Connect with us

SIYASA

Jam’iyyar PDP Ta Kaddamar Yakin Neman Zabenta a Jihar Katsina

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaban 2019 mai zuwa a matakin shugaban kasa da gwamna da kuma sauran masu neman mukami.
Da yake kaddamar da kwamitin dan takarar gwamna a karakashin jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina, Sanata Yakubu Lado Danmarke ya ce wannan kwamitin zai yi aiki hannun da hannu da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar Katsina.
Ya kuma bayyana cewa yanzu jam’iyyar ta su a dunkule take, saboda haka suna fatan samun nasara a dukkanin zabubbuka masu zuwa, kuma kwamitin guda daya ne sai dai zai yi aiki tare da sauran kwamitocin domin haka ta cimma ruwa.
Haka kuma ya kara da cewa nan ba da jimawa ba, zai fito da tsare-tsaren da yake da su wadanda zai bayyanawa mutanen jihar Katsina, tare da fatan cewa idan ya samu nasara zai cika alkawarin da ya dauka.
Shima da yake nasa jawabin shugaban jam’iyyar PDP a jijar Katsina, kuma dan takarar mataimakin gwamna, Honorabul Salisu Yusuf Majigiri ya ce suna da tabbacin mutanen jihar Katsina PDP za su zaba.
Sai dai a cewarsa, ba za su yi amfani da kalmar nan ta ‘Sak’ ba saboda wai ‘yan Najeriya ba su ji dadinta ba, “mu dai a namu takin shi ne tun daga sama har kasa PDP ce ba ruwan da wannan kalma ta ‘Sak’ domin bata haifar da alheri ba. in ji shi.
Kazalika ya bayyana mutanen da ke kunshe cikin dabtarin kudin kwamitin yakin neman zaban, wanda sun wuce mutun dari uku amma dai ya ce akwai kwamitoci guda takwas da za su yi aiki tare.
Ya kuma bayyana wasu daga cikin jiga-jigan kwamitin da za su aikin yakin neman zaban tun daga matakin shugaban kasa har zuwa dan majalisar jiha kamar haka;
Alhaji Sani Abu Minista shi ne babban darakta na yakin neman zaban sai Dakta Garba Shehu Matazu a matsayin darakta mai kula da shiyar Funtua sai kuma Alhaji Namadi Dankama da zai jagorancin yankin Katsina ta tsakiya
Akwai Alhaji Abubakar Bindawa (Mai Gemu) zai shugabanci yankin Daura, a yayinda Lawal Rufa’I Safana zai kasance a matsayin sakataran kwamitin yakin neman zaban sannan akwai Hajiya Bilkisu Kai kai a matsayin shugabar Mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!