Connect with us

SIYASA

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe Ya Ajiye Mukamin Sa

Published

on

Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Hon Adamu Dala Dogo, ya rubuta takardar ajiye mukamin sa na kakakin zauren majalisar, yanzu da rana.

 

Hon Dogo wanda ya dauki tsawon shekaru bakwai (7) ya na jan ragamar majalisar dokokin jihar Yobe.

 

Takardar ajiye mukami, ta kashin kan sa, ta samu karbuwar baki dayan mambobin zauren majalisar, wanda kuma nan take aka nada sabo- wanda aka nada Hon. Zanna Ali.

 

Hon Zanna Ali wanda shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Machina. Inda kuma nan take aka rantsar da Alh. Zanna Ali, a matsayin sabon kakakin majalisar, a gaban baki dayan mambobin majalisar.

 

Har wa yau kuma, Hon Zanna Ali ya bayyana cewa zai ci gaba daga inda tsohon kakakin majalisar ya tsaya tare da shan alwashin cewa, zai kyautata yaukin alakar majalisar da bangaren zartaswar jihar, saboda bunkasa manufofin gwamnatin jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!