Connect with us

HANGEN NESA

Kano Ta Tsakiya: Kalubalen Da Ke Gaban Malam Shekarau

Published

on

Tsohon Gwamnan jihar kano na shekara takwas ya gama kewaye-kewayen sa na jam’iyya, tare da neman gurin zama, a yanzu dai Malamin yasamu jam’iyyar APC har kuma sun sahhale masa tsayawa takarar Sanatan KANO ta tsakiya, wato dai kujerar da abokin adawarsa zai bari, tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma Sanatan dake kai a yanzu, duk da cewa banda fin karfi da a kai wa Shekaran, zuciyarsa tafi karkata zuwa takarar Shugaban kasa kamar Kwankwasan, amma dole kanwar naki, yanzu ya zubar da wadancan makaman, ya canza zuwa Sanatan kano ta tsakiya, bayan Kwankwaso yayi kutun-kutun ya wancakalar dashi a jam’iyyar ta PDP da suka hadu, dama can masu sharhin siyasa na ganin auren da masu adawar suka hada a PDP, sunan sa rababbe, tuni kuwa hakan ta tabbata, an raba gari, kowa ya ja dagarsa.
Fitowar Malam Shekarau din neman kujerar Kwankwaso, hakan ya kara zafin adawar Shuwagabannin biyu, bayan dinkewa da Malamin yayi da Gwamna Ganduje, wanda a yanzu babban burin Mai jar hular ya wancakalar da Gwamnan daga kan kujerar sa.
Duk da farin jini da masoya da Malam Shekarau yake da su a jihar kano, amma tabbas akwai babban kalubale agabansa wajen lashe wannan kujera, musamman ganin zai yi takara ne da dan gaban goshin Kwankwaso, kuma Dan Majalisar tarayya maici a yanzu na Dala, Aliyu Madakin Gini, hakan na nuna akwai babban aiki ja wajen ganin Malam Shekarau ya kayar da jam’iyyar PDP, kuma babban abokin adawar sa a siyasance.

•KaYar Da Jam’iyyar PDP
Adawa da jam’iyyar PDP ba karamin abu bane, duk da cewa masu hasashe na ganin shi kansa Aliyu Madakin tura shi aka yi yayi wannan takarar, yayin da wasu ke ganin ta yaya dan Majalisar tarayya zai iya kada tsohon gwamna, wanda yake da tarin masoya. Wadannan abubuwa sune kalubalen dake gaban Shekarau tashi tsaye wajen neman yakin zabe, tare da amfani da tsofaffin mutanen sa wadanda suka kware a siyasa, hakan ne kadai zai iya sanyawa ya iya kada PDP.

•Wane irin ayyuka Zai yi talla da su?
Al’umma sun dangwalawa Kwankwaso ruwan kuri’u wajen hayewa kan Sanatan, amma babban abin mamaki shi ne, yadda Kwankwason ya zama me dumama kujera kawai a majalisar, babu wasu kudurorin kirki da za ka ce Kwankwason ya shigar wadanda za su amfani mazabarsa, ko jiharsa koma kasar baki daya, ya zama tamkar bebe a majalisar, ya zama kawai dan eh da a’ah ne. Dole ne Shekarau ya san wasu irin kudurori ne zai yi talla da su har mutane su sahhale masa, su kuma yadda shi ma ba zai yi irin yadda abokin adawar tasa yayi ba, akwai bukatuwar kudurori da al’ummar Kano ta tsakiya suke bukata musamman ta bangaren aikin inganta kasa da kuma ruwan sha, idan har shi ma ya rasa manufofi masu mahimmanci, to lalle ko da ya haye, za a maimaita ‘yar gidan jiya ne.
Lura da Bukatu da damuwar al’ummar mazabun kano ta tsakiya.
Al’umma na ganin Sanata Kwankwaso bai maida hankali akan al’amuran mazabun da yake wakilta ba, tamkar ya je tallata hajarsa ta jar hula da takarar Shugaban kasa ne, hakan ya sanya ya manta akwai wasu al’umma da yake wakilta, hakan ya janye masa hankali wajen ziyarar mutanen sa tare da sauraren kokensu, hakan ne kadai hanyar da Shugaba na kwarai zai gane bukatun mutanen sa, sannan zai gani da idanuwansa abubuwan da suka cancanta ya kai gaban majalisa don biyawa al’ummar sa bukatun su, ko kuma zartar da wata doka da za ta amfani mutanensa. Hakan babban kalubale ne gaban Malam Shekarau don ganin bai mai da Abuja tamkar nan ne mahaifar saba, kamar yadda mai jar hular yayi, dole ne ya kasance me ziyartar al’ummar sa tare da jin kokensu da zai je gaban Dattijai ‘yan uwansa ya zayyana, tare da tabbatar da cewa an biya musu bukatun su.

Wakiltar al’umma ba tallan kai ba.
Yana daga cikin abubuwan da suka kara nuna rashin amfanin Kwankwaso a majalisar Dattijai, yawace-yawacen tallar takarar sa. Tabbas Malam Shekarau har kawo yau yanada burin kara tsayawa takarar Shugaban kasa, idan har ya maimaita irin abinda Kwankwaso ya aikata, hakan zai kashe duk wata nasarar sa da kuma burin sa, domin hausawa na cewa ba’a gudu kuma ana susar baya, zai yi batan bakatantan, shi baiyi wa al’umma abinda yadace ba, sannan baiyi nasarar cimma kudurin saba.
Rashin Dogara da wani Shugaba.
Babu ko tantama al’umma na ganin har kawo yau babu kyakykyawar alaka tsakanin Shekarau da Buhari, wanda hakan har yaso bawa takarar tasa matsala. Dole ne Shekarau ya fito yayi tallar kansa ba tare da rabewa da wani ba, tuni hakan ya zama kauyanci a siyasa, amfani da wani a cimma nasara, dole ne ya bugi kirji yatsaya kai da fata ganin ya farantawa kowa ba tare da ganin cewa idan yana tare da wane ba zai yi nasara ba, ko sai da wane zai yi nasara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!