Connect with us

LABARAI

Kasafin Kudin 2019: Gwamnatin Adamawa Ta Gabatar Da Sama Da Naira Miliyan 230

Published

on

A jiya talata ne, gwamnan jihar Adamawa Umaru Bindow Jibrilla, ya gabatar da naira miliyan dubu dari biyu da talatin da dari tara, da tamanin da tara da dubu hudu da goma sha biyu, da dari uku da saba’in da biya (N230, 989 412, 375), gaban majalisar dokokin jihar.
Kasafin wanda gwamnan ya ce an yiwa take da “Kasafi Mai Cike Da Fata” ya samu karfafawa daga kasafin kudin shekarar 2018.
Gwamna Bindow ya ci gaba da cewa “kasafin shekarar 2019, zai maida hankali wajan samar da ayyuka, bunkasa harkar noma, Kiwon lafiya, ilimi da samar da ruwansha mai tsafta.
“dama ni gwamnan talakawa ne, wannan kasafin kai tsaye talaka zai amfana dashi, zamu bunkasa ilimi, sake gina asibitoci da samar da ruwa da kyautata harkar noma.
“saboda haka muka mika wannan kasafi ga majalisa, wadda shine irinsa na farmo mai yawa, dake cike da fata ga jama’ar jihar Adamawa” inji Bindow.
Haka kuma gwamnan ya kuma yiwa majalisar bayanin cewa za’akashe naira miliyan dubu dari da uku, da miliyan dari hudu da tasa’in da biyar, da dudu dari biyu da talatin da tara, da dari biyar da saba’in da biyar, wajan kyautata rayuwar jama’a.
Ya ce gwamnatinsa zata kuma kashe wasu naira miliyan dubu dari da ashirin da bakwai da miliyan dari hudu da casa’in da hudu, da dubu dari da saba’in da shida da dari daya (N127,494,176,100), a manyan ayyuka.
To sai dai tuni majalisar ta yiwa kasafin karatu na biyu, lamarin da kakakin majalisar Kabiru Mijinyawa, ya ce sun yi hakan ne domin ganin kasafin ya fara aiki nan da karshen wannan shekarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!