Connect with us

KASASHEN WAJE

Kasashen Duniya 193 Za Su Mara Baya Ga Shirin Dakile Kaurar Baki

Published

on

Wakilan wasu kasashen duniya 70 sun amince su yi aiki tare don magance matsalar kwararar baki, matakin da ke nuna goyan bayan shirin Majalisar Dinkin Duniya wanda wasu kasashe suka janye daga ciki.
Yayin da duniya ke fama da matsalar baki Yan gudun hijira sama da miliyan 21, daukacin kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya banda Amurka, sun amince da wani daftari a watan Yuli da zai taimaka wajen dakile kwararar baki da kuma kula da su yadda ya kamata.
A taron da zai gudana tsakanin ranakun gobe Litinin da jibi Talata a Morocco, ana saran wakilan kasashen duniya sun amince da daftarin, duk da ya ke wasu kasashen Turai da suka fada karkashin ikon ‘yan ra’ayin rikau irin su Austria da Hungary da Poland na adawa da shirin.
Wasu Magadan Gari da suka halarci taron da ya gudana a Marakesh a karshen mako, kamar na Saliyo Ybonna Aki-Sawyerr da Marbin Rees na Bristol da ke Birtaniya sun bayyana muhimmanci cimma yarjejeniya domin shawo kan matsalolin da ke haifar da kaurar jama’a. Daftarin ya yi bayani kan yadda za’a taimakawa bakin da suka bar kasashen su saboda dalilai masu karfi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!