Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Barcelona Za Ta Siyar Da Dembele?

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ousmane Dembele ya sake makara a filin daukar horon kungiyar bayan daya kara awanni biyu akan yadda ake fara daukar horo a kungiyar.
Dembele, wanda yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka jefa kwallo a raga a wasan da kungiyar ta Barcelona ta lallasa kungiyar Espanyol daci 4-0 bai bada dalilin dayasa ya aikata hakan ba.
A kwanakin baya ma dai dan wasan yaki zuwa filin daukar horon kungiyar inda kuma da aka tambayeshi sai yace cikinsa ne yayi ciwo duk da cewa kungiyar kwallon kafar ta Barcelona bata yarda da uzurin nasa ba.
Rashin zuwa filin daukar horo akan lokaci da Dembele yakeyi dai shine babbar matsalar dan wasan da shugabannin kungiyar kuma akan haka kungiyar tabbas zata iya rabuwa da dan wasan saboda bazata yarda da halaye marasa kyau daga wajen dan wasa ba.
Dembele yakoma kungiyar Barcelona ne a kakar data gabata sai dai a kakar wasansa ta farko yasha fama da ciwo wanda hakan yasa bai samu damar buga wasanni dayawa a kungiyar ba kuma a wannan kakar ma baya buga wasa akai-akai saboda halayensa na makara a dilin daukar horo.
Kungiyoyin Liverpool da Arsenal da PSG ne suke zawarcin dan wasan wanda yakoma Barcelona daga kungiyar Dortmund kuma kungiyar ta siyeshi ne domin ya maye mata gurbin Neymar, wanda kungiyar ta siyar zuwa PSG.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!